Manyan Malamai Sun Fayyace Hukuncin Crypto da ‘Mining’ a Addinin Musulunci

Manyan Malamai Sun Fayyace Hukuncin Crypto da ‘Mining’ a Addinin Musulunci

  • Mansur Ibrahim Yelwa ya yi bayani mai gamsarwa a kan abin da ya shafi hukuncin Mining a addinin musulunci
  • Shehi kuma malamin jami’ar ya saurari bayanai daga wadanda suka kware a harkar, sai ya ba da fatawa a addini
  • Limamin babban masallacin Abuja, Ibrahim Ahmad Maqary ya yi magana a kan mas’alar tare da ba matasa shawarwari

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A karatunsa na littafin Al Muhararr fil Hadith, Mansur Ibrahim Yelwa ya yi magana a kan hukuncin Mining da kirifto a musulunci.

Bayanin ya zo ne bayan kammala karatu a kan babin sallah a ranar 20 ga watan Mayu 2024 ganin yadda hankalin mutane ya karkata.

Mining
Malaman addinin Musulunci sun yi magana a kan Mining a Najeriya Hoto: @iam_safee, Bitcoin News, Nairametrics
Asali: TikTok

Sheikh Yelwa ya halatta Mining

Kara karanta wannan

Notcoin: Dan Najeriya ya samu Naira miliyan 9 daga haƙar ma'adanan crypto a wayarsa

Malamin ya ce mutane da yawa sun yi masa tambaya don haka ya ba da amsa saboda a hutar da sauran malamai daga wannan batu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan sauraron zancen masu harkar, Farfesa Mansur Ibrahim Yelwa ya ce mining ya halatta saboda mutum yana amfani da guminsa.

Salon Mining da aka fito da su yau

An bijiro da tambaya a kan staking, sai ya ce a duba salon idan ya yi kama da bashin banki ko kuma zuba jari domin a juya a kamfani.

A wajen karatun, malamin ya ji bambancin mining da aka saba da shi da kuma farming.

Malam ya nuna hakan zai halatta idan ana neman jawo karin mutane da za su rungumi wannan salon kasuwanci da aka shigo da shi ne.

Da ya saurari bayanin Future trading, Sheikh Mansur Yelwa ya kamanta shi da caca, ya kuma ce ba zai halatta a addinin musulunci ba.

Kara karanta wannan

Yayin da ya ke jimamin mutuwar mahaifiyarsa, Kotu ta tausayawa Abba Kyari

Farfesan ya ce ya halatta a ajiye kudi bayan an saida sulallan mining, amma dole idan za a yi ciniki a yi musayar kudi ba tare da jinkiri ba.

Mining: Sheikh Maqary ya ce ayi hatarra

Shi kuwa Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary ya ce mining bai cikin tushe a addini, kuma zai iya zama halal ko haramun a wasu lokutan.

Limamin babban masallacin na Abuja ya ce ya sabawa salon da aka sani wajen neman kudi a al’ada, amma hakan bai nufin ya haramta.

Sheikh Ibrahim Ahmad Maqary ya ba matasa shawara su rungumi silar nema na kwarai kamar yadda za a ga bayanin a shafin Facebook.

"Mining yana cikin aiyukan Wasa'il, ba Maƙasid ba.
Zai iya zama Halal ko Haram gwargwadon abubuwan da ke tattare dashi, da abinda zai kai zuwa gareshi.
Koda yake ya saɓa da hanyoyin, da Musulunci ya tsara na neman kudi, amma ba za a, iya cewa Haramun bane yanke.

Kara karanta wannan

Hallaccin 'Mining': Abin da malamin musulunci ya ce game da Notcoin da TapSwap

Sai dai, ina baiwa Matasa shawara, su shagalta da nagartattun hanyoyi masu amfani, cikin ginin Addini da Rayuwa wajen neman kudinsu."

- Ibrahim Ahmad Maqary

Sheikh Zarewa zai yi magana kan Mining

Dazu kun ji labari Sheikh Jamilu Yusuf Zarewa yana son sanin shin mining wani wasa ne ko kuma nema ne da jibin-goshi da aka kawo.

Malamin fikihun ya bayyana cewa kafin a yi hukunci za a so sanin shin yawan danne-dannenka ne yawan sulallar da ake samu a Mining.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel