Garabasa ko Son Banza: Yadda Matashi Ya Maida Hankali, Ya Samu Miliyoyi da Crypto

Garabasa ko Son Banza: Yadda Matashi Ya Maida Hankali, Ya Samu Miliyoyi da Crypto

  • Taf! Taf!! Taf!!! Ita ce karar da yanzu ake yawan ji daga matasa masu rike da babbar waya a wani kokari na yin 'mining' domin samun kudin crypto idan ta fashe
  • Tun bayan fashewar Not Coin (NOT) a makon da ya gabata ne matasan Arewacin Najerya su ka rungumi harkar 'mining' da gaske a wani yunkuri na tara abun duniya
  • Injiniya Abubakar AY Danmari, kwararren 'dan crypto da ya fara harkar tun a shekarar 2022 ya bayyana cewa ana samu, amma mining din wannan karon ba zai fashe nan kusa ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - A makon da ya gabata ne matasa da yawa a Arewacin kasar nan su ka samu kudin ba zata bayan fashewar 'mining' din Not Coin (NOT).

Kara karanta wannan

Hallaccin 'Mining': Abin da malamin musulunci ya ce game da Notcoin da TapSwap

Bayan wannan lokaci ne maza, mata da manya su ka rungumi 'mining' da gaske domin wadanda ba sa amfani da kafar nan ta 'Telegram' da yawa yanzu sun yi rajista domin fara 'crypto'

Kudin Crypto
Matasa a Arewa sun rungumi harkar 'mining' da gaske Hoto: Alistair Berg
Asali: Getty Images

Matashi ya samu kudi da Crypto

Injiniya Abubakar AY Danmari, matashi ne a Kano da ya mallaki dukiyoyin miliyoyin Naira ta hanyar crypto, ya bayyana cewa yadda matasa suka tsunduma ‘mining’ yanzu ba shi ne zai sa su samu kudin da suke hari ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ‘mining’ da ake yi yanzu na dan lokaci ne kamfanonin crypto ke yi domin tara mabiyan da za su taimaka wajen cika bukatun bude kamfanin su tsaya a kafafunsu a kasashen Turai.

Yadda Crypto ta hana Danmari NYSC

Tun bayan fara crypto a shekarar 2002, matashi Abubakar AY Danmari ya bayyana cewa ya kammala karatu a lokacin da iliminsa na sanin harkar crypto ya yi nisa.

Kara karanta wannan

Ba a manta da kisan Ummita a Kano ba, wani ɗan China ya sake kashe ‘yar Najeriya

A cewarsa, ubangidansa a wancan lokaci wani dan kabilar Ibo ne, kuma a lokacin ya fara samun kudi mai tarin yawa da ya sa shi canza shekarunsa saboda ka da ya shiga shirin hidimar kasa (NYSC).

Ya ce a lokacin ya na samun akalla $500 duk wata, wanda hakan ya sa ya ga ba zai iya shiga NYSC ba, ya yi asarar kudin.

"Crypto ba za ta hana ka karatu ba, akwai dai bangaren da mutane ke shiga da zai iya hana ka karatu saboda hidimar da ke ciki."
''Yanzu haka ina daukar nauyin iyali na da yan uwana mutum takwas, da iyaye na."

Akwai haramtaccen crypto a Musulunci

Bangaren 'futures trading' shi ne bangaren da wasu malamai suka bayyana a matsayin haramtacciyar hanyar samun kudi.

Abubakar AY Danmari ya bayyanawa Legit Hausa cewa a wannan bangaren ne mutum zai iya tashi ba ko sisi, an kwashe, ko kuma ya wayi gari da kudi mai tarin yawa.

Kara karanta wannan

'Dan Tik Tok ya kashe kansa bisa kuskure a idon mabiyansa wajen yin bidiyo

Danmari, wanda daya ne daga jagororin masu yin crypto a jihar Kano ya ce malamai sun haramta futures trading, saboda tsarin addinin musulunci bai amince da shi ba.

Abubakar AY Danmari ya bayyana cewa akwai bangarorin crypto da dama, kamar cinikayya da saye da sayarwa, saboda haka a shawarci matasa su nemi ilimin crypto kafin tsunduma cikinsa.

'Ba son banza ba ne,' matasan Kano

Khadija Isma'il Ahmad matashiya ce mai kimanin shekaru 30 a jihar Kano, ta shaidawa Legit Hausa cewa ta yi da-na-sanin kin yin 'ming' din notcoin, saboda haka za ta dage.

Ta ce gwamnati ta gaza nemawa 'yan Najeriya mafita, tunda yanzu sun samu za su rike ta hanni bibbiyu.

Shi ma Saddam Musa Khalid matashin magidanci ne, kuma ya ce ya shiga 'mining' ne domin gwada sa'arsa, ba don son banza ba.

Ammar Wakili wanda notcoin ta fashe da shi, ya ce ya sayi takin zamani domin yin noma, saboda haka yanzu ya shiga wasu 'mining' din irinsu tapswap da Cex.io saboda akwai alheri a ciki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kaddamar da mummunar hari a Plateau, an kashe mutane 40

Duk matasan da Legit tatattauna da su na ganin mafita ce ta zo ga talakawan matasan Najeriya.

'Crypto na taimakawa ta'addanci:,' EFCC

A baya mun ba ku labarin cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta bayyana cewa ana amfani da 'crypto' wajen daukar nauyin ta'addanci.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana haka, inda ya ce sun gano cewa ana amfani da shafuka irinsu Binance wajen hada-hadar kudin ta'addanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel