An Shiga Jimami a Kaduna Bayan Gwamna Uba Sani Ya Tafka Babban Rashi

An Shiga Jimami a Kaduna Bayan Gwamna Uba Sani Ya Tafka Babban Rashi

  • An shiga jimami bayan rasuwar kanin Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna a jiya Juma'a 24 ga watan Mayu
  • Gwamnan ya sanar da mutuwar kaninsa inda ya nuna alhini a jiya Juma'a 24 ga watan Mayu a shafinsa na X
  • Gwamnan ya kwatanta marigayin, Mukhtar Lawal Isma'il a matsayin mutum mai ƙan-ƙan da kai da kuma himma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya sanar da babbar rashi da ya yi na kaninsa.

Gwamnan ya yi jimamin mutuwar kaninsa mai suna Mukhtar Lawal Ismail a daren jiya Juma'a 24 ga watan Mayu.

Uba Sani na Kaduna ya tafka babban rashi a rayuwarsa
Kanin Gwamna Uba Sani ya kwanta dama a jiya Juma'a. Hoto: Uba Sani.
Asali: Facebook

Uba Sani ya kaɗu da rasuwar kaninsa

Kara karanta wannan

InnalilLahi: An shiga jimami yayin da ɗan Majalisa mai-ci ya rasu a Adamawa

Uba Sani ya nuna alhini kan rasuwar Mukhtar inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai himma da kokari da kuma kan-kan da kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Uba Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na X a jiya Juma'a 24 ga watan Mayu.

"InnalilLahi wa inna ilaihir rajiun, cikin mika lamari ga Ubangiji ina sanar da rasuwar kanina Pharm. Mukhtar Lawal Isma'il."
"Marigayin ya kasance mutum mai ƙan-ƙan da kai da himma da kuma kwarewa a layinsa, tabbas za mu yi kewarsa."
"Allah ya gafarta masa ya saka shi gidan aljanna firdausi mu kuma masoyansa ya bamu hakurin jure rashinsa."

- Uba Sani

Dattijo Gidado Bello Akko ya rasu

Har ila yau, Allah ya yi wa shahararren marubuci, Gidado Bello Akko rasuwa a jiha Lahadi, 19 ga watan Mayu.

An yi jana'izar tsohon ma'aikacin wanda ya kasance daga cikin dattawan jihar Gombe a Zariya da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

"Ina godiya Abba": Sarki Sanusi II ya magantu bayan dawowa kujerarsa

Dan majalisa a Adamawa ya rasu

A wani labarin, kun ji cewa an tafka babban rashi bayan rasuwar wani ɗan Majalisar jihar Adamawa, Abdulmalik Jauro Musa.

Marigayin wanda ya wakilci mazabar Ganye a jihar ya rasu ne da safiyar jiya Juma'a 24 ga watan Mayu a India.

Jauro Musa kafin rasuwarsa, shi ne mataimakin shugaban masu tsawatarwa na bangaren marasa rinjaye a majalisar da ke cike da mambobin PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel