Dawo-Dawo: An Sanar da Sabon Sarkin Kano, Sanusi Ya Zama Sarki a Karo Na Biyu

Dawo-Dawo: An Sanar da Sabon Sarkin Kano, Sanusi Ya Zama Sarki a Karo Na Biyu

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana Malam Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon Sarkin Kano bayan rushe masarautu biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta kirkira
  • Wannan na zuwa ne bayan tsige basaraken a shekarar 2020 bisa yawan sabani da ake samu tsakanin gwamnatin Ganduje da Sarkin, wanda ake zargi da rashin biyayya da ladabi
  • Tun bayan shan rantsuwa da Abba Kabir Yusuf ya yi a watan Mayun 2023 ake ta sa ran dawo da maganar yiwa dokar da ta kafa masarautun Kano kwaskwarima, amma hakan bai yiwu ba sai yau

Jihar Kano-Yanzun nan aka sanar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kano shekaru bayan tsige shi.

Wannan na zuwa ne bayan da majalisar dokokin jihar ta tabbatar hade masarautun jihar guda biyar da tsige dukkan masu rike da mukaman.

Kara karanta wannan

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga mayar da Sanusi II gidan sarauta

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ne ya ayyana Malam Muhammadu Sunusi II a matsayin sarkin Kano.

Gwamnati ta umarci sarakuna su bar masarautu

A yammacin yau Alhamis ne Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci sarakunan Kano da aka tube guda biyar su bar masarautunsu nan da awanni 48.

A sanarwar da darakta janar kan yada labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na facebook, ya ce sanya hannu kan dokar tambar dawo da martabar Kano ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tabbatar da cewa yanzu Kano na karkashin masarauta guda daya tal, kamar yadda aka sani a shekarun baya.

"Kowa ya ci gaba da ayyukan gabansa yadda ya saba, mun aiwatar da abin da muke ganin shi ne masalaha ga kowa," inji sanarwar.

Primetimes News ta wallafa cewa haka kuma Gwamna Abba gida-gida ya umarce su da mika dukkannin kayan gwamnati dake hannunsu ga ma'aikatar kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Gwamna Abba ya mayar da Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano

Gwamna Fubara ya taya Sarki Sunusi murna

A baya mun kawo muku labarin cewa Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya taya Mai martaba sabon sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II murnar komawa karagarsa.

Malam Muhammadu Sunusi II ya samu labarin sake nada shi sarkin Kano na 16 yayin taro kan tattalin arziki dake gudana a jihar Rivers.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel