Jami'an DSS da Ƴan Sanda Sun Mamaye Zauren Majalisa Yayin da Rigama Ta Kaure

Jami'an DSS da Ƴan Sanda Sun Mamaye Zauren Majalisa Yayin da Rigama Ta Kaure

  • Rikicin da ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Kuros Riba ya ja hankalin jami'an tsaro yayin da DSS da ƴan sanda suka dira wurin
  • Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun mamaye majalisar ne bayan tsige kakakin majalisar, Elvert Ayambem daga kan muƙaminsa
  • 17 daga cikin mambobi 25 ne suka kaɗa kuri'ar tsige shugaban majalisar bisa zargin yin sama da faɗi da wasu maƙudan kuɗi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Jami'an hukumar tsaron farin kaya (DSS), ƴan sanda da wasu jami'an tsaro sun mamaye zauren majalisar dokokin jihar Kuros Riba.

Jami'an tsaron sun ɗauki wannan matakin ne bayan tsige shugaban majalisar, Elvert Anyambem, a zaman yau Laraba, 22 ga watan Mayu, 2024.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya faɗi yadda suka shirya tsige sarakuna 5 da Ganduje ya naɗa a Kano

Jami'in DSS.
Jami'an tsaro sun kai ɗauki majalisar dokokin Cross River bayan barkewar rikici Hoto: Patrick Meinhardt
Asali: Getty Images

'Yan majalisar dokoki sun kusa yin fada

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ƴan majalisar sun kusa ba hammata iska yayin da rigima ta ɓarke bayan tsige Ayamben daga muƙaminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakamakon haka ne jami'an DSS, ƴan sanda da wasu dakarun hukumomin tsaro suka dira majalisar domin tabbatar da doka da oda, rahoton jaridar Vanguard.

Ayamben mai wakiltar mazaɓar Ikom II ya rasa muƙaminsa na shugaban majalisar bisa zarginsa da sama da faɗi da wasu maƙudan kuɗi.

Elvert Ayambem ya mayar da martani

Sai dai Honorabul Ayamben ya ce bai tsigu ba, yana nan daram a kujerarsa ta shugaban majalisar dokokin jihar Kuros Riba.

A wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar, ya bayyana abin da ya faru ranar Laraba a matsayin abin ban dariya da ba shi da tushe a kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun ɗauki mataki da majalisa ta fara gyara dokar masarautun Kano

A rahoton Channels tv, Ayamben ya ce tsige shi da ake ta yaɗa wa duk jita-jita ce kawai mara tushe.

Sanarwar ta ce:

"Honorabul Elvert Ayambem ne kakakin majalisar Kuros Riba, babu mai ja da haka a yanzu.
"Abin da ya faru yau a zaman majalisa lokacin da Effiong Akarika, mamba mai wakiltar Kalaba ta Kudu 1 ya kawo hargitsi a majalisar abun dariya ne mara tushe."

Majalisa ta fara gyara dokar Ganduje

A wani rahoton kun ji cewa Ɗan majalisar dokokin Kano ya bayyana cewa tun ba yanzu ba suka so tsige sarakunan masarautu biyar da Abdullahi Ganduje ya kirkiro.

Ya faɗi haka ne yayin da ƴan majalisar suka fara zaman garambawul ga dokar masarautun da Ganduje ya yi amfani da ita wajen tsige Muhammadu Sanusi II.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel