Majalisar Kano Za Ta Gyara Dokar da Ganduje Ya Yi Amfani da Ita Wajen Tsige Sanusi II
- A zamanta na yau Talata, majalisar dokokin jihar Kano ta fara aikin yiwa dokar Sarakunan Kano kwaskwarima
- Shugaban masu rinjaye kuma mai wakiltar mazabar Dala, Hussien Dala, ya gabatar da kudirin a gaban majalisar
- An fara gyara dokar ne a 2019 a lokacin da ake takun saka tsakanin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano na 14
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta fara aikin yiwa dokar Sarakunan Kano kwaskwarima a daidai lokacin da ake kira da a dawo da tsohon Sarkin Kano na 14, Muhammad Sanusi.
Majalisar ta yanke shawarar gyara dokar ne bayan shugaban masu rinjaye kuma mmai wakiltar mazabar Dala, Hussien Dala, ya gabatar da kudirin a yau Talata.
Mai taimakawa gwamnan Kano, Hassan Tukur ya tabbatar da haka a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gyara dokar sarkakunan jihar Kano
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an fara gyara dokar ne a shekarar 2019 a lokacin da ake takun saka tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Sarkin.
Gyaran da aka yi na farko ya raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar, inda aka kirkiro masarautu na Rano, Karaye, Gaya da Bichi.
Haka zalika, an nada sarakuna masu daraja ta daya ga sababbin masarautun, wanda a karshe ya kai ga tsige Sarkin Kano na lokacin.
Kano: An nemi dawo da Sarki Sanusi
Amma bayan nasarar zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf, kungiyoyi da dama sun yi kiraye-kiraye ga majalisar jihar da ta dawo da Sarki Sanusi.
Wata guda kafin Gwamna Yusuf ya hau kan karagar mulki, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano, ya ce za a sake duba batun masarautun.
Dalilin tsige Sarki Sanusi a Kano
Tun da fari, mun ruwaito cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II a watan Maris din 2019.
Wata sanarwa da sakataren gwamnatin Kano na wancan lokaci, Alhaji Usman Alhaji, ta ce Sarki Sanusi ya nuna halin rashin biyayya ga wasu umurni da Ganduje ya bayar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng