Sabbin sarakunan yanka: Jerin kananan hukumomin da zasu kasance a karkashin sarki Sanusi II

Sabbin sarakunan yanka: Jerin kananan hukumomin da zasu kasance a karkashin sarki Sanusi II

Biyo bayan amincewa da kirkirar sabbon masarautu hudu da majalisar dokokin jihar Kano tayi a ranar Laraba, mai martaba sarki Muhammadu Sanusi II zai kasance yana da iko a kananan hukumomi 8 daga cikin 44 da jihar Kano keda su.

A kudirin kirkirar sabbin masarautun na farko dake gaban majalisar, an bar wa masarautar Kano kananan hukumomi 10, amma bayan majalisar ta mika kudirin ga kwamitin ta, sun rage yawan kananan hukumomin zuwa guda 8.

A sabuwar dokar da majalisar ta amince da ita, sarki Sanusi zai kasance yana da iko da kananan hukumomin Kano Municipal, Tarauni, Dala, Nasarawa, Fagge, Gwale, Kumbotso da Ungoggo.

Karin masarautu hudu da majalisar ta kirkira sune; Bichi, Rano, Gaya da Karaye.

Sabbin sarakunan yanka: Jerin kananan hukumomin da zasu kasance a karkashin sarki Sanusi II
Sarki Sanusi II da Ganduje
Asali: Twitter

Majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin kakakin majalisar Rt. Hon Alhassan Rurum ta amince da kafa sababbin masarautu guda hudu a fadin jihar Kano.

DUBA WANNAN: Zanga-zanga a gidan minista: 'Yan daba sun tarwatsa mambobin NLC

"Ba a samu wadanda suka nuna rashin amincewar su ba a dakin majalisar. Sai dai akwai wadanda suka dinga fita daga majalisar wadanda alamu ke nuna cewa ba su ji dadin dokar ba," wani dan majalisar wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyanawa manema labarai cewa.

A yanzu haka dai ana shirin mika dokar wajen Mai Girma Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, domin ya rattaba hannu akan dokar wacce za ta share hanya akan nadin sababbin sarakunan Kano na yanka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel