Kannywood: Muna shan wahala matuka wajen samun mazajen aure – Rashida Abdullahi
Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood kuma 'yar siyasa mai suna Rashida Abdullahi ta jadadda cewa suna fuskantar kalubale wajen samun mazajen aure.
Majiyarmu ta kawo inda Jarumar ta kara da cewa: “Samun Mazan Ne Da Wahala, Amma Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Za Tayi Aure”.
Idan zaku tuna Legit.ng ta kawo a baya cewa jarumar dai ta janye kafar ta daga fitowa a matsayin jaruma a cikin fina-finan Hausa na Kannywood sannan kuma ta tsunduma cikin harkokin siyasa.
KU KARANTA KUMA: An rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomi a Kano
A yanzu haka ma har ta samu mukamin mai bayar da shawara ga Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng