Bamu Zabi Peter Obi Ba: Kiristocin Arewa Sun Watsawa Babachir Lawal Kasa a Ido

Bamu Zabi Peter Obi Ba: Kiristocin Arewa Sun Watsawa Babachir Lawal Kasa a Ido

  • Shugabannin Kirstocin Arewa na jam'iyyar APC sun nesanta kansu daga Babachir David Lawal
  • Kungiyar Kiristocin sun ce ba da izininsu ya sanar da zaben dan takaran shugaban kasan Labour Party, Peter Obi ba
  • Babachir Lawal, wanda shine shugaban kungiyar ya sanar da cewa sun yi ittifakin marawa Peter Obi baya

Abuja - Sanarwar da Babachir David Lawal yayi na wanda Kiristocin Arewacin Najeriya zasu marawa baya ya bar baya da kura.

Shugabannin kungiyar Kiristocin Arewa na jam'iyyar APC sun nesanta kansu daga marawa dan takaan jam'iyyar Laboru Party, Peter Gregory Obi, baya.

Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, wanda shine shugaban kungiyar ya ce Peter Obi za su yi.

Amma manyan mabiyansa Kiristoci sun juya masa baya.

Dogara
Bamu Zabi Peter Obi Ba: Kiristocin Arewa Sun Watsawa Babachir Lawal Kasa a Ido Hoto: Mr. Peter Obi, Rt. Hon. Yakubu Dogara
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Saboda Tsabagen Girmamawa, An Sanyawa Titi Sunan Muhammadu Buhari a Kasar Waje

Ba damu akayi hakan ba, Yakubu Dogara

A wasikar kar-ta-kwana da suka fitar da daren Alhamis, 24 ga Nuwamba, mambobin kungiyar kimanin goma karkashin jagorancin tsohon Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara sun yi hannun riga da Babachir.

Sun bayyana cewa marawa Peter Obi baya ra'ayinsa ne kawai kuma ba na kungiyarsu ba, rahoton Leadership.

Dogara ya ce har yanzu suna kan yanke shawara kan wanda zasu marawa baya a zaben.

A cewarsu:

"Yanke shawara kan dan takaran da zasu marawa baya da shugabanmu ya sana ra'ayinsa ne kawai kuma ba na kungiyarmu ba."
"Muna kyautata zaton cewa wannan zai zama fashin baki game da tambaye-tambayen da mutane ke yi kan ra'ayinmu."

Tikitin Musulmi da Musulmi: Tinubu Da Shettima Ba Za Su Dandana Mulkin Najeriya Ba a 2023, inji Babachir Lawal

Babachir Lawal, ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) da dan takarar, Asiwaju Tinubu Bola ba za su kai labari ba a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Lawal ya ce Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba zai yi nasara a zabe mai zuwa ba saboda zaban Kashim Shettima musulmi dan uwansa da yayi a matsayin abokin takara.

Babachir ya bayyana hakan ne a wani hira da yayi da sashen Hausa na BBC.

Ya tuhumi Tinubu da watsi da Kiristocin Arewa kuma yana ganin ko babu su zai isa lashe zaben shugaban kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel