Dakarun soji sun dakile harin kwanton bauna, sun kashe 'yan ta'adda 2 a Borno (Hotuna)
Domin tabbatar da ababen hawa sun cigaba da zirga-zirga da jigila a dukkan titunan da ke fadin jihar Borno da yankin arewa maso gabas, rundunar soji ta 26 ta gudanar da wani atisaye ranar Asabar inda har ta fafata da wasu mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai musu wani harin kwanton bauna.
Dakarun sojin sun fafata da 'yan ta'addar ne a lokacin da suka raka ayarin motocin 'yan kasuwa a kan hanyarsu ta zuwa kauyen Wala da makwabtan kauyuka. Mayakan da ke cikin matsanancin bukatar kayan abinci da ragowar kayan amfani, sun kai wa tawagar harin kwanton bauna domin samun ganimar kayan abinci.
A jawabin da mukaddashin darektan yada labarai da hulda da jama'a na rundunar soji, Kanal Sagir Musa, ya fitar, ya ce: "dakarun soji sun mayar da martani nan take bayan mayakan sun kawo harin kwanton bauna, an yi musayar wuta mai zafi, amma daga bisani dakarun soji sun dakile harin tare da kashe biyu daga cikinsu da kuma kwace bindigunsu kirar AK47 guda biyu.
"Bayanan sirri da mu ka samu daga baya sun tabbatar mana da cewa 'yan ta'addar sun samu labarin zuwan tawagar sojoji da fararen hula 'yan kasuwa ta hannun masu basu bayanai a kan motsin rundunar sojoji.
"Sun so yin amfani da wannan damar wajen kai hari a kan dakarun sojoji tare da yin awon gaba da kayan abinci da ragowar kayan masarufi da su ke matukar bukata.
"Domin kara tabbatar da tsaro bayan dakile harin, an kara tura wasu rundunonin sojoji zuwa yankin domin cigaba da sintiri.
"A cigaba da sintirin ne dakarun soji su ka gano wasu sinadarai masu fashe wa (IEDs) da mayakan su ka binne a hanyoyin yankin. Dakarun mu sun samu nasarar kwance bama-baman ba tare da sun tashi ba.
DUBA WANNAN: Mata na 3 da yara 11 - Mai garkuwa da mutane ya fadi nasarorin da ya samu
"Duk da barazanar fashewar sinadaran da mayakan su ka binne, rundunar sojoji ta cigaba da kutsa wa zuwa cikin yankin tare da kwance karin wasu sinadaran. Ba a samu asarar rai ko samun rauni ba a bangaren rundunar sojoji ba yayin aikin" a cewar sanarwar.
Kanal Musa ya kara da cewa, sintirin sojojin na daga cikin atisayen 'HALAKA DODO' da rundunar soji ke yi a karkashin babban atisayen 'Ofireshon LAFIYA DOLE' a jihar Borno.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng