Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa

Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana daya daga cikin manya-manyan 'yan siyasan Najeriya

- Sannan Buhari yana daya daga cikin manya-manyan masu dukiyar Najeriya, ba zaka sani ba sai ka bincika

- Cikin wannan labarin akwai tarihin Buhari, dukiyar da ya tara, iyalinsa, karatunsa da komai na rayuwarsa

Muhammadu Buhari babban dan siyasa ne a Najeriya, kuma yanzu haka shugaban kasa. Ya mulki Najeriya tsakanin 1983 zuwa 1985 a matsayinsa na soja.

An kuma zabe shi a matsayin shugaban kasa na mulkin farar hula a 2015, kuma ya zarce a 2019. Kafin zabensa, ya rike manyan makamai a kasar nan.

Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa
Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa. Hoto daga Drew Angerer
Asali: Getty Images

An haife shi a 17 ga watan Disamban 1942 a karamar hukumar Daura dake jihar Katsina. Yanzu haka, shekarunsa 78 da haihuwa. Iyayensa Fulani ne, mahaifinsa, Hardo Adamu, mahaifiyarsa kuma Zulaihat.

Buhari shine da na 23 a wurin mahaifinsa. Mahaifinsa ya rasu yana da shekaru 4 da haihuwa, sakamakon haka, mahaifiyarsa tayi ta dawainiya dashi.

KU KARANTA: Hotunan tsuleliyar budurwa da ta zama likita sun gigita samari, suna mika kokon bararsu

Buhari ya fara karatunsa ne a Mai'adua da makarantar firamare ta Daura kafin ya shiga Katsina Middle School a 1953.

Bayan nan, ya zarce Katsina Provincial Secondary School, tukunna ya shiga makarantar horarwa ta sojoji (NMTC) a 1962. Tsakanin 1962 da 1963 yaje Cadet Training dinsa a Mons Officer Cadet School a Aldershot dake Ingila.

Buhari yana daya daga cikin wadanda suka yi wa Yakubu Gowon juyin mulki, sakamakon haka aka daura shi a matsayin gwamnan jihar Borno na mulkin soji, wanda da ake kira jihar arewa maso gabas.

Sannan a wannan shekarar, janar Olusegun Obasanjo ya zabe shi a matsayin kwamishinan tarayya na man fetur.

A 1977, Buhari ya zama sakataren Supreme Military Headquarters. Sannan ya rike kwamandan sojoji na Kaduna.

An yi wani juyin mulki a 31 ga watan Disamban 1983, wanda aka daura Buhari a matsayin shugaban kasan Najeriya. Ya dauki tsauraran matakai akan masu karbar rashawa.

KU KARANTA: Sallamar hafsoshin tsaro: Mutane basu hango abinda Buhari yake hange, Garba Shehu

Buhari ya fara harkar siyasa ne a 2003, lokacin da yayi takara da Olusegun Obasanjo na shugabancin kasa, amma ya kayar dashi karkashin jam'iyyar PDP.

Ya kara tsayawa takara a 2007, amma Umaru Yar'Adua na PDP ya kayar da shi.

Sannan sun tsaya takara da Goodluck Jonathan a 2011, amma bai samu nasara ba. Sai a 2015 ne da ya tsaya takara karkashin jam'iyyar APC ya samu nasara. Ya zarce Jonathan da kuru'u miliyan 2.5. An nada shi a kan karagar mulki a 29 ga watan Mayun 2015.

Ya samu nasarar samun kuru'u 56%.

An karrama Buhari a wurare mabambanta, ciki har da Defence Service Medal (DSM), Congo Medal (CM), General Service Medal (GSM), Grand Commander of the Federal Republic of Nigeria ( GCFR), Global Seal of Integrity (GSO).

Buhari ya yi aurensa na farko ne a 1971, inda ya auri Safinatu Yusuf. Sun haifi yara 5, Zulaihat (marigayiya), Fatima, Musa (marigayi), Hadiza da Safinatu. Auren Buhari ya kare da Safinatu a 1988.

Ya auri matarsa ta biyu bayan rabuwarsa da ta farkon a watan Disamban 1989. Matarsa, Aisha Buhari, tana da yara 5, Aisha, Halima, Yusuf, Zahra da Amina.

Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa
Shugaba Buhari a 2021: Cikakken tarihi, dukiyar da ya tara, shekaru, ilimi da iyalinsa. Hoto daga muhammadubuhari
Asali: UGC

Buhari yana daya daga cikin attajiran Najeriya. A 2021, an kiyasta cewa ya mallaki dala miliyan 110. Buhari yana daya daga cikin masu dukiyar kasar nan tun daga lokacin da yayi mulkin soji har zuwa yanzu.

A wani labari na daban, The Nation ta ruwaito yadda Kwamared Didi Adodo, tsohon kwamishinan kwadago da ayyuka na musamman na jihar Edo ya rasu.

Shugaban kwadagon ya mutu ne da safiyar Talata, 12 ga watan Janairu, bayan fama da cutar COVID-19 na tsawon kwanaki.

Tsohon kwamishinan ya rike kujerar sakataren ISSSAN kafin rasuwarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng