Albashin shugabanni da 'yan majalisun dattijai da na wakilan tarayya

Albashin shugabanni da 'yan majalisun dattijai da na wakilan tarayya

An dade ana tafka muhawarra kan albashi da allawus din 'yan majalisar Najeriya. Akwai rahotanni da dama da suka wallafa mabanbantan adadin kudin da 'yan majalisar ke dauka a duk shekara.

Duk da haka, muhimman abu a nan shine korafin da ake yi na cewa 'yan majalisar Najeriya suna daga cikin wadanda ke karbar albashi mai yawa a duniya har ma fiye da wasu takwarorinsu na kasashen da suka cigaba.

A 2015, Quartz Africa ta rubuta wani rahoto da ya ce 'yan majalisar Najeriya suna daga cikin wadanda suka fi daukan albashi mafi tsoka a duniya kuma ta gabatar da alkalluma daga The Economist domin kare wannan ikirarin.

A 2018, tsohon dan majalisa, Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana cewa dan majalisa na karbar N750,000 a matsayin albashi duk wata tare da naira miliyan 13.5 a matsayin allawus jimla ya kama naira miliyan 14.25 duk wata.

Shin nawa ne ainihin albashin dan majalisar Najeriya? Legit.ng ta yi bincike kan albashi da allawus din da 'yan majalisar Najeriya ke karba duk wata.

Shugaban Majalisar Dattawa

Kamar yadda wani takarda da 'Revenue Mobilisation, Allocation and Fiscal Commission' (RMAFC) ta wallafa a bpsr.gov, albashin shugaban majalisar dattawan Najeriya a shekara shine N8,694,848:75 (N8.69m) yayin da albashinsa na wata kuma N722,570:72

Ga kiddidigar albashin na shugaban majalisar dattawa da allawus dinsa kamar yadda RMAFC ta wallafa.

Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Asali: UGC

Mataimakin Shugaban Majalisa

Mataimakin shugaban majalisar dattawa albashinsa na shekara shine 8,082,083:65 (N8.0m) yayin da albashinsa na wata kuma N673,507:00.

Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Asali: UGC

Sauran Sanatoci

Albashi da allawus din sauran sanatoci na shekara guda kamar yadda RMAFC ta wallafa shi N12,766,320:00 (N12.7m). Albashi da allawus din su na wata kuma shine N1,063,860:00 (N1.06m).

Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Abba vs Ganduje: Kotun koli ta ki amincewa da bukatar da Ganduje ya gabatar

Albashin Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya

Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya yana karbar 4,954,220:00 (N4.95m) duk shekara, a kowane wata kuma yana daukan N412,851:66 amma banda allawus.

Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Asali: UGC

Albashin sauran 'Yan Majalisar Wakilan Tarayya

Albashin sauran 'yan majalisar wakilai na tarayya a cewar RMAFC a shekara shine N9,529,038:06 (N9.5m) yayin da albashnsu na wata kuma shine N794,086:83.

Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Abinda sanatoci da 'yan majalisar tarayyar Najeriya ke dauka a matsayin albashi da allawus
Asali: UGC

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164