“Za a Fara Jigila a Jirgin Kasan Lagos Zuwa Kano a Watan Yuni” in Ji Ministan Tinubu
- Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa layin dogo da aka gina daga Legas zuwa Kano zai fara aikin jigilar kayayyaki a watan Yunin 2024
- Hakan ya fito fili ne a yayin wata ziyara da ministan sufuri, Saidu Alkali ya kai zuwa jihar Kano domin duba cigaban aikin layin dogon
- Kamfanin China da ya yi aikin ya bayyana cewa an hada layin dogon da tashar jiragen ruwa ta tsandauri da ke Zawaciki a Dala da ke Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano – Ministan sufuri, Saidu Alkali ya ce za a fara jigilar kaya a kan layin dogo na Legas zuwa Kano a watan Yuni 2024.
Kamar yadda Voice of Nigeria ta ruwaito, Sa'idu Alkali ya kai ziyara inda ake gudanar da aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu.
Minista ya fadi tasirin dogon Lagos-Kano
An tattaro cewa wani kamfanin gine-gine na kasar Sin; China Civil Engineering Construction Corporation (CCECC) aka ba aikin gina layin dogon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin na CCECC ya sanar da cewa an hada layin dogon har zuwa tashar jiragen ruwa ta tsandauri da ke Zawaciki, Dala a birnin kasuwanci na Kano, inji jaridar Leadership.
Sanata Alkali ya ce idan layin dogon ya fara aiki, zai tsawaita karkon manyan titunan Najeriya tare da rage yawan mutanen da ke mutuwa a hatsarin mota.
"Za a kammala dogon Kano-Daura" - Alkali
Channels TV ta kuma ruwaito ministan ya yi karin bayani kan raba aikin zuwa kashi-kashi domin tabbatar da aiwatar da shi cikin sauki da kuma saurin kammala shi.
"Na tattauna da dan kwangilar, za mu raba aikin kamar haka; Kano zuwa Daura za a kammala a shekara mai zuwa, Daura zuwa Maradi a 2026 da kuma Dutse zuwa Kano a 2026."
- Sa'idu Alkali.
Fara aikin jigilar kaya a kan layin dogo daga Lagos zuwa Kano ya nuna wani gagarumin ci gaba da za a samu a harkar sufurin Najeriya, wanda zai tabbatar da tsaron kayayyaki.
Za a kaddamar da titin Abuja-Kaduna-Katsina
A wani labarin, mun ruwaito maku gwamnatin tarayya ta ce za a kammala aikin titin Abuja-Kaduna-Katsina daga nan zuwa karshen shekarar 2025.
Ministan ayyuka, David Umahi, wanda ya bayyana hakan a lokacin da gwamnan Kaduna, Uba Sani ya kai masa ziyara ya ce kamfanin Dangote, BUA da Julius Berger ne aka ba aikin.
Asali: Legit.ng