Gwamnatin Buhari ta kulla yarjejeniyar fara aikin layin dogo daga Ibadan zuwa Kaduna

Gwamnatin Buhari ta kulla yarjejeniyar fara aikin layin dogo daga Ibadan zuwa Kaduna

A ranar Talata, 15 ga watan Mayu ne gwamnatin tarayya da kamfanin kasar China, CCECC suka rattafa hannu akan yarjejeniyar gina titin jirgin kasa na zamani daga garin Ibadan na jihar Oyo zuwa jihar Kaduna, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an kulla yarjejeniyar ne akan kudi dala biliyan 6.68, inda aikin wani sashi ne na gina babbar hanyar jirgin kasa na zamani da gwamnati ta dauki aniyar ginawa tun daga jihar Legas zuwa Kano.

KU KARANTA: Azumin watan Ramadana: An yi kira ga Malamai game da zage zage yayin fassara Al-Qur’ani

Kaakakin ma’aikatan watsa labaru na ma’aikatar sufuri, Yetunde Sonaike ce ta bayyana haka, inda tace: “wannan wani sashi ne na aikin titin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano, kuma ana sa ran kammala aikin Ibadan-Kaduna cikin shekaru uku.”

Gwamnatin Buhari ta kulla yarjejeniyar fara aikin layin dogo daga Ibadan zuwa Kaduna
Jirgin kasa

Sanarwar ta kara da cewa Ministan ma’aikatan sufuri, Rotimi Amechi ya bada tabbacin ma’aikatarsa za ta kammala biyan nata Kason kudin da za’a gudanar da aikin a cikin kasafin kudin shekara mai zuwa.

Hakazalika layin dogon zai ratsa garuruwan da suka hada da Oshogbo-Illorin-Minna zuwa Kaduna. Tun a shekarar 2006 ne aka fara aikin Legas zuwa Kano, inda aka rarraba aikin don saukaka shi a shekarar 2008, an fara aikin ne daga Kaduna zuwa Abuja, wanda a shekarar 2016 ya fara aiki.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel