Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dira Zawaciki, jihar Kano

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dira Zawaciki, jihar Kano

  • Bayan kammala na Legas-Ibadan, za'a fara layin dogon Kano-Kaduna
  • Shugaba Buhari da kansa zai kaddamar da fara ginin a yau
  • An fara bukin kaddamarwa yanzu haka a jihar Kano

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira garin Zawaciki, inda aka shirya kaddamar da fara ginin layin dogo daga jihar Kano zuwa jihar Kaduna.

Ministan Sadarwa, Dakta Isa Ali Pantami ya bayyana cewa gwamnoni da Ministoci tuni sun dira garin kuma suna saurarin zuwan shugaban kasan ne.

Za’ayi tashohin jirgin kasa a Kaduna, Jaji, Zaria, Kwakwa, Madobi da Kano.

Mun kawo muku a baya cewa, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis zai kaddamar da fara ginin layin dogon jirgin kasa na Kano zuwa Kaduna.

Sakataren din-din-din na ma'aikatar sufuri, Dr Magdalene Ajani, ta bayyana hakan a jawabin da ya saki a Abuja ranar Talata.

KU KARANTA: Gwamnan Bauchi: Na san wadanda ke daukan nauyin masu garkuwa da mutane

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dira Zawaciki, jihar Kano
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dira Zawaciki, jihar Kano
Asali: Facebook

KU DUBA: Fasto ya karkatar da N15m na coci don karatunsa na PhD

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dira Zawaciki, jihar Kano
Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dira Zawaciki, jihar Kano Hoto: Dalafm
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel