Jiragen kasa na Legas zuwa Kano zasu ci gaba da aiki
Wani ruhotu a jiya ya bayyana cewa Jirgin kasa na Legas zuwa kano da ya daina aiki bayan wani rushewar hanyoyi na hanyar jirgin kasan a ƙasar Neja zai fara aiki
Kamfanin Railway Corporation na Najeriya (NRC) ya kammala aikin gyare-gyare a kan gadan da ya rushe a yayin da ake sa ran za a sake dawo da aikin fasinjoji a mako mai zuwa.
Daily Trust ya kawo ruhotu cewa an dakatar da ayyukan kwasan fasinjoji na Legas zuwa Kano da kuma kayan sufuri na abubuwa daban-daban daga Legas zuwa Kano bayan wankewar wata hanyar jirgin kasa a Jihar Neja.
Kafin gyaran sashen hanyar jirgin, jiragen kasa ba ya iya tafiya da kaya daga Legas, babban birnin kasuwancin kasar sai dai ya tsaya a Jihar Kwara.
A yanzu komai zai dawo daidai ma masu tafiya ta hanyar jirgin kasar da kuma NRC tunda yanzu an kammala aikin gyare-gyaren da akeyi, yayin da jirgin kasan ya fara kwasan kaya.
KU KARANTA KUMA:A kama Nnamdi Kanu ko mu dakatar da aiyukkan gwamnati a Abuja - Kungiyar AYA
Amma duk da haka an fahimci cewa hidimar mako-mako daga Legas zuwa Kano ba zai ci gaba a yanzu ba sai mako mai zuwa.
Babban Darakta na NRC, Mista Niyi Ali ya tabbatar wa wakilinmu cewa an gyara duk hanyar da ta lallace.
Ya ce, jirgin da ke tafiyar Lagos zuwa Kano ya kasance a Kano lokacin da lamarin ya faru,jirgin zai tashi zuwa Legas a ranar Litinin don fara aiki na musamman.
"An kammala aikin gyara. Muna da cikakken hanyar jirgin Legas zuwa Kano,"in ji shi.
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng