Aikin dogon jirgin Legas zuwa Kano ya kankama –Ministan sufuri, Amaechi

Aikin dogon jirgin Legas zuwa Kano ya kankama –Ministan sufuri, Amaechi

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa an fara aikin titin dogon da za ayi daga Legas har zuwa jihar Kano a Arewa maso yammacin kasar nan.

Mai girma Ministan sufuri na kasa, Rt. Hon. Rotimi C. Amaechi ya bayyana cewa an fara sashen wannan aiki daga yankin Kaduna zuwa garin Kano.

Ministan ya tabbatar da wannan ne ta shafinsa na Twitter@ChibuikeAmaechi kamar yadda jaridar Vanguard ta fitar da rahoto a ranar 22 ga watan Yuli, 2020.

Kwanakin baya dama ministan ya yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta sa hannu domin a fara wannan aiki da zai hada bangororin kasar biyu.

Rotimi C. Amaechi ya bayyana cewa ‘yan kwangila sun isa yankin dauke da manyan kayan aiki. Za a kammala wannan dogo cikin shekaru uku idan an samu kudi.

Tun a shekarar 2006, a gwamnatin Olusegun Obasanjo aka fara maganar wannan titin dogon mai tsawon kilomita 305, sai yanzu ne ake sa ran aikin zai tabbata.

KU KARANTA: Buhari ya fi kowane shugaban kasa farin jini a Twitter

Aikin dogon jirgin Legas zuwa Kano ya kankama –Ministan sufuri, Amaechi
Ministan sufuri da tawagarsa
Asali: Facebook

A 2018 ne gwamnatin Najeriya ta shiga yarjejeniyar Dala biliyan 6.68 da kamfanin CCECC na kasar Sin domin ayi wannan titin jirgin kasa na Kano zuwa Legas.

A wancan lokaci an shirya cewa za a fara aiki a watan Mayun bana, amma dole aka dakata zuwa tsakiyar shekara a sakamakon annobar COVID-19 da ta barke.

Mun samu labari shugaban kasa ya bada umarnin ayi maza a fara wannan aiki kafin watan Satumba, kuma kamfanin da aka ba wannan kwangila ya ji wannan umarni.

Kasar Sin za ta narka Dala biliyan 5.3 a cikin wannan aiki, yayin da Najeriya za ta biya 15% na kudin kwangilar. Yanzu Sin ta soma bada Dala biliyan 1.6 domin aikin ya kankama.

A na ta bangaren, Najeriya za ta fitar da Dala miliyan 318 na aikin a wannan shekara, zuwa shekarar 2021 kuma za a saki wasu kudin kamar yadda minister ya fada.

Mutane sun dade su na kiran gwamnatin Buhari ta fara wannan gagarumin aiki. Ana ma sa ran nan gaba a soma aikin dogo tun daga Fatakwal har zuwa Maiduguri.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel