FEC ta yarda a kashe Naira Tiriliyan 5 domin gina jirgin kasa tun daga Legas har zuwa Kalaba
- FEC ta yarda a kashe Dala biliyan 11.17 a aikin jirgin kasan Kalaba zuwa Legas
- Za a kai 2027 ana wannan gagarumar kwangila da za ta ci har Naira Tiriliyan 5
- Gwamnatin Tarayya ta yarda za ta saye 20% na hannun jarin matatar Dangote
Abuja - Majalisar zartarwa ta kasa, FEC, ta amince a kashe fam Dala $11.17 domin a ayi aikin gina titin jirgin kasa daga jihar Legas zuwa garin Kalaba.
Za a fadada hanyoyin dogo a Najeriya
The Cable ta ce za a gama wannan aiki da zai hada garuruwan da suke kusa da ruwa a shekaru shida.
Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed ya sanar da hakan bayan an kammala taron FEC da aka saba yi duk mako a fadar shugaban kasa.
Lai Mohammed ya ce Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya gabatarwa FEC da takardu biyu da za su taimaka wajen fadada hanyoyin jiragen kasa a Najeriya.
“Na farko ya shafi aikin titin jirgin kasan garin Kano zuwa Jibia, na biyu kuma ya na magana ne a kan titin jirgin kasan Fatakwal zuwa garin Maiduguri.”
“A yau majalisa (FEC) ta bada dama a soma yin aikin titin jirgin Legas zuwa Kalaba.”
Rotimi Amaechi ya ce gwamnatin baya ta amince da wannan aikin, amma ba ta yi komai a kai ba.
Titin jirgin Legas zuwa Kalaba zai ratsa garuruwa 15
Titin zai ratsa Legas zuwa Sagamu, Sagamu zuwa Ijebu-Ode, Ijebu-Ode zuwa Ore, Ore zuwa Benin, Benin zuwa Sapele, Sapele zuwa Warri, Warri har Yenogoa, Yenegoa zuwa Fatakwal, Fatakwal zuwa Aba, Aba zuwa Uyo, Uyo zuwa Kalaba, Kalaba har Akamkpa zuwa Ikom, sai Obudu.
Za a samu tasha a Benin, Agbo, Ogwashi-ukwu, Asaba, gadar Onitsha, Fatakwal, da tashar Onne.
Jaridar This Day ta ce majalisar FEC ta kuma amince gwamnatin tarayya ta mallaki 20% na hannun jari a matatar man da Aliko Dangote yake gina wa a Legas.
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci taron na FEC da aka yi a ranar Laraba, 4 ga watan Agusta, 2021, tun da shugaban kasa ba ya Najeriya.
Hakan na zuwa ne a lokacin da ake jin cewa MTN Nigeria zai dauki nauyin gyaran hanyar Onitsha zuwa Enugu Gwamnatin Tarayya ta yafe wa kamfanin haraji.
Rahotanni sun tabbatar da cewa MTN Nigeria ya amince ya shiga tsarin RITC da gwamnati ta shigo da shi domin a gyara wasu hanyoyi ko gina tituna a kasar nan.
Asali: Legit.ng