Yadda Matsalar Ruwa Ke Haifar da Wahalar Rayuwa a Arewacin Najeriya
- Duk da bilyoyin kudade da gwamnatoci ke ikirarin kashewa wurin samar da ruwa, matsalar ruwa ta addabi garuruwa da dama a Arewa
- A wannan karon lamarin ya yi kamari lura da yadda matsalolin rashin wuta da tsadar man fetur suka kara dagula al'amura a yankin
- A wannan rahoton, Legit ta tattauna da mutane da dama a garuruwa mabambanta domin jin halin da suke ciki a wannan yanayi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
A yayin da aka shigo lokacin zafi a mafi yawan garuruwan Arewacin Najeriya kuma aka fi bukatar ruwa domin sha da wanka da saauransu, matsalar ruwa ta kara ta'azzara.
Hakan yana kuma da alaka ne da rashin samun wuta, karin kudin lantarki da wahalar man fetur har ma da tsadarsa.
A yankin Arewa maso gabashin Najeriya, ana fiskantar matsalar ruwa da ba a taba ganin irin ta ba sakamakon lalata layin wutar lantarki da bata gari suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rashin wuta ya haifar da matsalar ruwa
Dama dai galibin mutanen yankin sun dogara ne da ruwan da ake hakowa daga bohol mai amfani da lantarki.
A yayin da aka samu matsaloli sun dabaibaye harkar wutar lantarki, komai sai ya tsaya cak, ruwa ya zama zuma; samunsa sai dan gata.
A wasu yankunan kuma, duk da cewa akwai wutar amma ba kowa ke samunta ba saboda sai wadanda suke layin Band A ne suke da lantarki a mafi yawan lokuta..
Wata babbar matsala ita ce ko da akwai wutar, ba kowa ne ke iya saya ba. Rijiyoyin burtsatsi kuɗi kuwa sun kara kudin ruwa saboda karin kudin wuta da man fetur.
Wuraren da ake fama da rashin ruwa
Legit ta tattauna da mazauna garuruwa mabanbanta a kan halin da suke ciki na matsalar ruwa a Arewacin Najeriya.
A jihar Adamawa, Legit ta yi hira da Fadimatu Usman, wace take zaune a karamar hukumar Gire a unguwar Wuro Hausa.
A cikin hirar, malama Fadimatu ta ce a yanzu haka, ba kowa ne ke samun yin wanka ba duk da halin zafin da ake ciki.
Idan mutum yana da yara da yawa kuma, to sai dai a zabi wadanda za a yi wa wanka yau da wanda za a yi wa gobe.
A cewarta, yara da manya na yin layi suna shiga lunguna domin neman ruwa, amma a mafi yawan lokuta haka suke dawowa batare da samu ba.
Ana wahalar ruwa a yankunan Kano
Haka labarin ya ke a jihar Kano kamar yadda Malam Musa Adamu Musa ya tabbatarwa Legit a lokacin da ta tattauna da shi.
Malam Musa ya labartawa jaridar cewa a yankin Dakata da 'Yankaba matsalar ruwa ta zama babban kalubale.
Ya ce, duk da tsananin bukatuwa da mutane suke da ruwa a wannan lokacin, farashinsa yana neman fin abin da mai karamin karfi ke samu a rana.
Hakan ya jefa al'umma da dama cikin kangi ta yadda hatta ruwan da za su yi amfani wurin ibada yakan gagara.
Babu isasshen ruwa a Gombe
A jihar Gombe kuwa, an shiga rashin ruwa da ba a taba ganin irinsa ba. Hatta wuraren da ake zuwa neman ruwa idan an shiga tasko babu.
Wani mazaunin unguwar Gabukka, Muhammad Ibrahim, ya labartawa Legit cewa a cikin Gombe ruwa ya dawo koda kudinka sai da rabonka.
Muhammad Abba Koli dake unguwar Dawaki ya fadawa Legit cewa sun shiga matsalar ruwa wacce basu taba gani ba, hatta tsarki da alola ma yanzu sai kana da kudi, saboda da ruwan leda suke amfani.
A Tudunwadan Pantami kuwa, Hamza Tukur ya labartawa Legit cewa a halin yanzu a cikin bohol da suke da su guda biyar, daya ne kawai ke iya sayan man fetur.
Saboda haka wurin kullum yana cike da hayaniya da tarin jama'a, koda kudinka idan ba karfi gareka ba to ruwa ya zama kwalelenka.
Matsalar ruwa a garuruwan Yobe
A garin Damaturu na jihar Yobe kuwa, nan ma dai matsalar ta yi kamari kamar sauran garuruwa da ke kewaye da ita
A hirar da Legit ta yi da Amina Muhammad, ta ce matsalar rashin ruwa ta shafi unguwanni da dama a Damaturu.
A cewar ta, matsalar ta kazanta a wurare irinsu Pampari, Nayinawa, Nasarawa, Abbari, Pawari Alansar da Gwange.
Wani ma'aikacin lafiya a asibitin Damaturu, ya shaidawa Legit cewa ko wankin shimfida ba a yi ba a wannan satin saboda rashin ruwa.
Farashin ruwa a garuruwan Arewa
A halin da ake ciki, farashin ruwa ya yi tashin gauron zabi a dukkan sassa na Arewa saboda karin kudin wuta da man fetur.
A Tudunwadan Pantami da ke Gombe kafin shiga wannan taskon, lita 120 bai wuce N200 zuwa N300 amma a halin yanzu, ya kai N1,000
Haka farashin ya ninka a jihar Kano, a yankin Dakata, farashin ruwa jarka daya ya haura daga N30 zuwa N100
A jihar Yobe ma haka abin yake, a baya ana sayan jarka 12 a N250 zuwa N300 amma a halin yanzu ya kai N800 zuwa N1,000
Tsadar fetur ya jawo tsananin rayuwa a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa karancin man fetur ya ƙara jefa mutane cikin ƙaƙanikayi a jihar Kaduna yayin da ƴan bunburutu suka fara cin kasuwa
Rahoto ya nuna cewa litar fetur ta kai N1,000 a hannun ƴan bunburutu kuma masu Napep da sauran ababen sufuri sun kara tsada
Asali: Legit.ng