Iyaye da Dalibai Sun Koka a Kan Sabon Tsarin Ba da Lamunin Karatun Gwamnatin Tarayya

Iyaye da Dalibai Sun Koka a Kan Sabon Tsarin Ba da Lamunin Karatun Gwamnatin Tarayya

  • Iyaye da ɗalibai sun koka a kan kwaskwarimar da gwamnatin tarayya ta yi wa sabon tsarin ba da lamuni ga dalibai
  • Shugaban kungiyar daliban jami'a ta kasa (NAUS), kwamared Obaji Marshall, ne ya magantu a kan canje-canje da gwamnati ta yi a cikin shekarar 2024
  • Ya nuna cewa akwai damuwa da barazana ga dalibai da ba shafaffu da mai ba wurin cire sharadin cancanta da gwamnatin ta yi a kan sabon tsarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Yayin da Iyaye da dalibai ke ci gaba da nuna damuwa a kan samun damar karatu da tsadar ilimi a Najeriya, sun yi kira ga gwamnatin tarayya a kan ta sake nazari kan kwaskwarima da ta yi wa sabon tsarin ba da lamuni wa dalibai.

Kara karanta wannan

NDLEA ta gargadi matafiya kan hanyar da ake iya aukawa cikin matsala

Students loan
Shugaban daliban jami'a, Obaji Marshall, ya ce ya kamata gwamnati ta tabbatar da adalci wurin ba da lamunin karatu. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Sun ce lalle akwai bukatar sake duba tsarin cikin gaggawa musamman idan aka lura da yadda dalibai da iyaye ke shan fama a harakar ilimi a fadin ƙasar da kuma halin rayuwar yau.

A farkon wannan shekararar ne dai shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar ba da lamunin karatu wa daliban gaba da sakandare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin da ya kawo shakkun lamunin karatu

Kwaskwarimar da aka yiwa dokar ya nuna za ta tabbatar da kafa asusun ba da lamuni a harkar ilimi tare da ba wa dalibai bashi amma an cire sharadin cancanta wanda ya kawo shakku ga iyaye da ɗalibai, cewar jaridar Leadership

Gwamnatin tarayya dai ta yi niyyar kaddamar da shirin ba da lamunin dalibai a cikin watan Satumba amma hakan bai samu ba.

Jinkirin ne ya kawo yi wa tsarin kwaskwarima wanda a halin yanzu ya jefa shakku wa iyaye da daliban bayan a karon farko sun yabi tsarin.

Kara karanta wannan

Babu tabbacin dawo da kudin tallafin wutar Lantarki Inji NERC

Lamunin karatu: Jawabin shugaban dalibai

Shugaban kungiyar daliban jami'a ta kasa (NAUS), kwamared Obaji Marshall ya yi kira da a tabbatar da adalci wurin ba da bashin.

Ya kuma kara kira da cewa dole a bawa tsarin kulawa sosai domin a tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne suke samun bashin ba wasu shafaffu da mai ba.

Ya ce hakan na da muhimmanci musamman lura da cewa an cire sharadin can-canta a cikin sharudan cin moriyar bashin.

Iyayen dalibai sun yi magana

A bangaren iyaye kuwa, Mista Joseph Chia ne ya ce sun dade suna jiran tsarin da zai saukaka musu hanyar ilmantar da 'ya'yansu kuma sun yi maraba da tsarin.

Amma dole gwamnati ta yi tsayuwar daka domin tabbatar da cewa wanda suka cancanta ne za su ci moriyarsa.

Tinubu ya magantu a kan bada lamunin karatu

A wani rahoton kuma, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa lamunin karatun dalibai zai fara aiki a shekarar 2024. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Litinin 23 ga watan Oktoba, 2023 a Abuja.

Ya yi bayanin ne yayin babban tataron tattalin arziki na kasa ya kuma ce wannan shiri na ba da lamuni ga dalibai zai taimaka wurin rage yawan yajin aiki a manyan makarantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel