Yadda Matsalar Wutar Lantarki ke Kara Kamari duk da Tsanantar Zafi a Najeriya

Yadda Matsalar Wutar Lantarki ke Kara Kamari duk da Tsanantar Zafi a Najeriya

  • Mazauna kasar nan, musamman masu kananan sana'o'i na bayyana takaicin yadda matsalar wutar lantarki ta ki ci ta ki cinyewa
  • Tun bayan da gwamnatin tarayya ta bayyana cire tallafin wutar lantarki da rarraba kwastomominta rashin wuta ya yi kamari
  • Kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ta nemi ministan lantarki na kasa, Adebayo Adelabu ya bayyana gabanta kan matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Nigeria - Tun bayan rarraba bangarorin samar da wuta a Najeriya, al’umma su ka kara kokawa kan yadda rashin wuta ke kokarin hana su gudanar da kananan sana’o’i, musamman a Arewa.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta yi gwanjon kamfanonin rarraba wutar lantarki 5, abubuwa sun lalace

Gwamnatin tarayya, ta hannun hukumar kula da wutar lantarki ta kasa (NERC) ce ta bayyana karin kudin wutar lantarki da kuma rarraba kwastomomi daga wadanda ke samun wuta daga awanni 20, wato ‘yan sahun band A da B.

Wutar lantarki
Matsalar wutar na durkusar da kasuwanci a Arewa Hoto: Getty Images
Asali: Facebook

Sauran wadanda ba sa wannan ajin kuma wutar sai abinda su ka gani, kamar yadda wata mai sana’ar sayar da lemuka ta shaidawa Legit Hausa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu kananan sana’o’in da matsalar ta fi shafa, musamman na jihohin da ke Arewa na ganin rashin wutar da ake fuskanta zai jefa sana’arsu cikin matsala.

Ga jerin wasu jihohin Arewa da matsalar rashin wuta ta yi wa kamari;

1. Kano

Mafi akasarin al’ummar jihar Kano, musamman na unguwannin Hotoro, sharada, Dorayi da kwaryar birnin Kano na fama da matsalar wuta.

Maman Areef, mazauniyar unguwar Kwari ce a Hotoron Arewa da ke karamar hukumar Nassarawa ta shaidawa Legit Hausa cewa sana’arta na sayar da kayan lemuka na neman durkushewa.

Kara karanta wannan

TCN: Ana kokarin gyara wutar lantarki bayan jihohi 3 sun shiga cikin Duhu

Ta shaida cewa:

“Wutar sai da daddare ake ba mu, kuma wutar daren ba sosai mu ke samu ba.”

Maman Areef ta kara da cewa:

“Yanzu abubuwan lemo ba na yi sosai, saboda yana lalacewa, sai dai ruwa, shi ruwa ba a asara.”

Ta ce a mako, wutar da su ke samu ba ta wuce awa a kullum.

2. Kaduna

Jihar Kaduna na daga wuraren da kae fama da matsalar wutar lantarki a Najeriya.

Matsalar wutar da ta fi nunawa da azumin Ramadana da ya gabata, an gano yadda aka dinga sayar da kankarar ruwa a kan Naira 400 zuwa 500.

A Zariya, sai da malaman addini su ka gagadi Gwamnatin tarayya ta yi kokarin wadata al’umma da wuta yayin da ake cikin matsanancin zafi.

Sheikh Salihu Shu’aibu Zariya ya yi kira ga kamfanoni DisCos da gwamnatocin jiha da tarayya su yi abinda ya dace saboda yanzu lamarin wuta ya tabarbare.

Kara karanta wannan

Kamfanin KEDCO ya yanke wutar asibitin Kano, masu haihuwa suna kwance

3. Gombe

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ta kasa (TCN) ya tabbatar da cewa mutanen Gombe na cikin duhu, duk da zafin da ake ciki. Sai dai kamfanin ya ce yana ƙoƙarin kawo gyarar wutar da ta lalace a jihar da wasu jihohin Arewa.

Ministan makamashi ya fadi dalilan rashin wuta

A watan Janairun shekarar nan, Ministan Makamashi, Cif Adebayo Adelabu ya dora laifin matsalar wutar akan karancin iskar gas.

Ta cikin sanarwar da hadiminsa, Bolaji Tunji ya fitar, ya bayyana cewa gwamnati na shirin biyan basussukan da ake binta domin samun karuwar iskar gas ga kamfanonin samar da lantarki.

Majalisa ta gayyaci hukumomin kan matsalar wuta

A wani rahoton da BBC Hausa ta wallafa a yau, kwamitin majalisar dattawa kan wutar lantarki ta nemi ministan lantarki na kasa, Adebayo Adelabu da hukumar kula da wutar lantarki ta kasa NERC su bayyana a gabanta saboda matsalar wuta.

Kara karanta wannan

'Yan sandan Kenya sun cafke shugaban kamfanin Binance da ya tsere a Najeriya

Shugaban kwamitin, Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce za su sanya hukumomin a gaba domin fayyace halin da rashin wuta da karin kudin wuta a kasar nan ke ciki.

Turakun wuta sun fadi karo na 6

A baya, kun ji turakun wutar lantarki na kasa sun sake faduwa karo na shida a bana, wanda ya sake jefa yan kasar nan cikin rashin wuta.

Tashar ta samu matsala ne da sanyin safiyar Litinin, inda kamfanin rarraba hasken wutar ya ce yana aikin gyara turakun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel