Gwamnan APC Zai Ɗauki Sababbin Ma'aikata Sama da 5,000 a Jiharsa, Ya Faɗi Dalili

Gwamnan APC Zai Ɗauki Sababbin Ma'aikata Sama da 5,000 a Jiharsa, Ya Faɗi Dalili

  • Gwamnatin Kuros Riba karkashin Gwamna Baseey Otu za ta ɗauki sababbin malamai 6000 domin cike giɓin rashin isassun malamai a makarantu
  • Kwamishinan ilimi na jihar, Stephen Odey, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a ofishinsa ranar Talata, 2 ga watan Afrilu
  • Ya ce hukumar tsaron farin kaya ta DSS tare da haɗin guiwar ƴan sanda na kokarin magance matsalolin ƴan asiri a makarantu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Cross River - Gwamnatin jihar Kuros Riba ta bayyana shirinta na daukar sababbin malamai 6000 sakamakon karancin malaman da ake fama da shi a makarantun jihar.

Stephen Odey, kwamishinan ilimi ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kalaba.

Kara karanta wannan

"Rashin ɗa'a": An fara zama kan batun tsige mataimakin gwamna, bayanai sun fito

Gwamna Bassey Otu na Cross River.
Gwamna Ottu zai ɗauki sabbin malamai 6,000 a Kuros Riba Hoto: Senator Bassey Otu
Asali: Twitter

Yayin wannan hira da ƴan jarida, kwamishinan ya jero wasu daga cikin nasarorin da ma'aikatar ilimi ta samu karkashin jagorancin Gwamna Bassey Otu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Gwamna Otu ya sake duba kudirin daukar karin malamai, inda ya ba da misali da yadda wasu makarantun ke da malamai hudu ko biyar kacal, cewar rahoton Daily Trust.

Haka zalika kwamishinan ya yi iƙirarin cewa wasu daga cikin ɓangarori da hukumomin da ke karƙashin ma'aikatar ilimi ba su da isassun ma'aikata.

Gwamnati za ta kula da walwalar malamai

Domin tabbatar da dorewar sha'awar aikin koyarwa da inganta harkar ilimi, Odey ya kuma bayyana cewa za'a samar da tallafi daban-daban ga malaman makaranta.

A cewarsa, gwamnati za ta maida hankali wajen ɗaukar malamai ƴan asalin yankunan da aka fi buƙatar ƙarin malaman, musamman yankunan karkara.

Ya ƙara da bayanin cewa wasu daga cikin malaman da aka rage wa matsayi saboda rashin kwalin karatu, za a ƙara masu matsayi bayan sun ƙaro karatu.

Kara karanta wannan

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda ya halaka kansa ta hanyar rataya

Da yake jawabi game da matsalolin ƴan kungiyoyin asiri a makarantu, Odey ya ce hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ‘yan sanda na kokarin yakar lamarin, The Cable ta ruwaito.

Majalisa ta tabbatar da bukatar gwamnan Kano

A wani rahoton na daban majalisar dokokin jihar Kano ta tabbatar da naɗin ɗan Kwankwaso da wasu mutum uku a matsayin sababbin kwamishinoni.

Shugaban majalisar, Isma'il Falgore, ne ya jagoranci tantance kwamishinonin a zaman majalisar na ranar Talata a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel