"Babu Zancen N1k": FG Ta Umurci UBA, Access Da Sauran Bankuna Su Bawa Kwastomomi Masu NIN Katin ATM Kyauta

"Babu Zancen N1k": FG Ta Umurci UBA, Access Da Sauran Bankuna Su Bawa Kwastomomi Masu NIN Katin ATM Kyauta

  • Gwamnatin tarayya ta umarci bankunan 'yan kasuwa da su bayar da katin cirar kuɗi (ATM) kyauta da zai zama katin shaidar ɗan ƙasa ga ‘yan Najeriya
  • Yanzu haka ‘yan Najeriya za su iya tambayar bankunansu da su ba su sabon katin cirar kuɗi na bai ɗaya
  • Sabon katin, zai yi aiki ne a matsayin katin shaidar ɗan ƙasa da kuma katin banki, kuma za a riƙa bayar da shi kyauta

Abuja - Gwamnatin tarayya ta umurci bankunan hada-hadar kuɗi da su bayar da sabon katin cirar kuɗi ga kwastomomin da ke da lambobin katin ɗan ƙasa (NIN).

Za a iya amfani da sabon katin wajen cire kuɗi daga na'urar cirar kuɗi (ATM), sannan kuma ayi amfani da shi a matsayin katin shaidar ɗan kasa.

Ministan sadarwa da tattalin arziki, Isa Pantami ne ya sanar da hakan a yayin da yake ganawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Sa Jamhuriyar Nijar Za Ta Kare Ni Idan Aka Matsa Min Bayan Na Sauka Daga Mulki, Buhari

FG ta umarci bankuna su bai wa kwastomomi ATM na bai daya kyauta
FG ta umarci bankuna su bai wa kwastomomi ATM na bai daya kyauta. Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Patanmi ya yi bayani kan sabon katin

A cewar Pantami, yanzu kowane ɗan Najeriya na iya tambayar bankinsa da ya ba shi sabon katin cirar kudin, kuma a kyauta kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan sabon katin ya bambanta da wancan na da wanda ake biyan kuɗi N1,000 a yayin karɓa ko sabuntawa.

Ya kuma bayyana cewa, matakin dai na zuwa ne bayan wata takardar da hukumar katin ɗan ƙasa ta ƙasa (NIMC) ta ba bankuna, wacce ta basu damar buga katunan cire kuɗi irin waɗanda kuma za su iya aiki a matsayin katin shaidar ɗan ƙasa.

Ministan ya bayyana cewa:

"Zai kasance wani nau'i na katin shaida na bai ɗaya, wanda zai yi aiki a matsayin katin shaidar ɗan ƙasa, a ɗaya hannun kuma ya yi aiki a matsayin katin banki, zai iya kasancewa katin Master, ko na Visa, ko ma kowane irin nau'in kati."

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Wani Dattijo Gidan Yari Saboda Sarrafa Kwandala Da Ficika Zuwa Kayan Ado A Kano

"Duk da cewa dokar NIMC ta shekarar 2007 ta tilasta wa 'yan Najeriya samun lambar shaidar ɗan ƙasa (NIN), ba lallai ba ne sai na kati ba, sai dai ana samun ƙaruwar masu buƙatar katin a faɗin kasar."

Pantami ya kuma bayyana cewa ‘yan ƙasa, musamman waɗanda ke zaune a yankunan karkara, kan ziyarci ofisoshin NIMC don nuna buƙatarsu ta samun katin ɗan ƙasar, duk da cewa ba dole ba ne.

Ya ci gaba da cewa:

“Don magance wannan matsala da kuma samar da sauƙi ga ‘yan ƙasa, NIMC ta bullo da katin shaidar zama ɗan ƙasa na zamani a shekarar da ta gabata, wanda za a iya saukewa ta hanyar manhajar NIMC.”

Katin zai yi aiki biyu, shaidar ɗan ƙasa da kuma cirar kuɗi

Pantami ya ce katin da za a bai wa mutum zai yi aiki biyu ne, aikin katin zama dan kasa, da kuma aikin katin cirar kudi.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe

"Duk da haka, tsarin ya ci-gaba da haifar da ƙalubale ga mutanen yankunan karkara. Domin magance waɗannan matsaloli, NIMC ta hada hannu da babban bankin Najeriya (CBN) domin bai wa ‘yan ƙasa da ke da sha’awa, damar samun katin ɗan ƙasa a bankunan su”.
"Bisa ga wannan umarni, an bai wa bankuna izinin buga katin, ko dai Mastercard ko Visa Card."
“Kati na bai ɗaya zai kasance a matsayin katin shaidar ɗan ƙasa da kuma katin banki, wanda zai kawar da bukatar katunan daban-daban. Abu mai muhimmanci shi ne, ba za a caji 'yan ƙasa ko sisi ba a yayin neman wannan sabon katin.”

Pantami ya kuma bayyana cewa duk wanda ke son irin wannan kati sai ya je bankinsa ya yi musu bayani cewa ga irin katin da yake so a yi masa.

Pantami ya fara shirye-shiryen barin ofis

A wani labarin da muka wallafa a baya, kun karanta cewa ministan sadarwa da tattalin arziƙi Farfesa Isa Ali Pantami ya fara shirin barin ofishinsa na minista da ke Abuja.

Hakan dai na zuwa ne a lokacin da ake shirye-shiryen rantsar da sabuwar gwamnati a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu da muke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel