Jerin Wasu Jihohin Arewacin Najeriya da Ke da Hukumar Hisbah

Jerin Wasu Jihohin Arewacin Najeriya da Ke da Hukumar Hisbah

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihohin Arewacin Najeriya da dama suna da hukumomin Hisbah da ke ba da agaji ko kuma dakile badala a jihohinsu.

Akwai wasu jihohi da har a Majalisar dokokinsu sun tabbatar da hukumar a cikin doka saboda taimakon al'umma.

Har ila yau, a wasu jihohin Hisbah kawai ta kasance ne a matsayin kungiya kamar ta agaji irin na sauran kungiyoyin addini.

Jihohin Arewacin Najeriya da suke da hukumomin Hisbah don taimakon Musulunci
Hukumomin Hisbah su na taimakawa wurin tabbatar da kawo sauyi a jihohi. Hoto: Aminu Daurawa, Muhammad Rabiu, Ahmed Daku.
Asali: Facebook

Misali a jihar Kano, Hukumar Hisbah ita ce mafi karfi a fadin Najeriya baki daya ganin yadda gwamnati ta saka hannunta a hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta jero muku wasu jihohin Arewa da suke da hukumomin Hisbah:

Kara karanta wannan

Duk da halin kunci da ake ciki, Kwastam ta sake cafke tirela makare da kayan abinci zuwa ketare

1. Kano

Hukumar Hisbah a kano ita ce mafi karfi a yankin saboda yadda gwamnati ke kula da hukumar da sauran ayyukanta.

Fitaccen malamin addini, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shi ke jagorantar hukumar da ta himmatu wurin yaki da badala a jihar.

Daurawa ya yi kokarin kawo sauyi a hukumar duk da matsalar da aka samu da ta tilasta shi yin murabus daga kujerar.

Daga bisani, Gwamna Abba Kabir ya yi zama da wasu manyan malamai da Daurawa inda aka samu maslaha tare da komawa kujerarsa.

2. Katsina

Jihar Katsina na daga cikin jihohin da ke da hukumar wacce ta ke da karfi ganin yadda gwamnan jihar ya nada sabon kwamandan jihar.

Gwamna Dikko Radda ya nada Ahmad Daku a matsayin shugaban Hukumar wanda shi ne tsohon gwamnan jihohin Kano da Sokoto a mulkin soja don kula da ayyukanta.

Kara karanta wannan

Daurawa: Ana tsaka da sulhu tsakanin Abba da Hisbah, hukumar ta samu babbar nasara

Hukumar a jihar ta na da matukar tasiri wurin dakile ayyukan badala da laifuka da dama a jihar.

3. Gombe

A jihar Gombe inda Sheikh Daurawa ke gudanar da tafsiri a ko wace shekara, hukumar ta yi karfi tare da jajircewar shugabanta, Malam Muhammad Rabiu.

Legit Hausa ta yi hira da kwamandan kungiyar a Gombe inda ya ce ya shafe shekaru 20 ya na jagorantarta yayin da ya yi shekaru biyu ya na mataimakin kwamanda.

"Mu Hisbah a Gombe muna karkashin kungiya ce da ke kula da sabbin Musulunta da kuma Da'awa wanda ayyukanmu ya sha bamban da sauran hukumomi a jihohi.
"Sannan muna sulhu tsakanin ma'aurata da makwabta da sauran ayyuka da suka shafi dukkan Musulmai idan su na bukatar agajinmu.
"Har ila yau, muna fadakarwa musamman ga matasa masu shaye-shaye ko zaman banza da sauran matsaloli."

- Muhammad Rabiu

4. Borno

Har ila yau, a jihar Borno akwai kungiyar Hisbah kamar ta jihar Gombe wacce aka yanke wa cibiya daga hukumar Hisbah a Kano.

Kara karanta wannan

Digiri kan Hisbah: Daurawa ya lissafa abubuwa 3 da za su yi a inganta aikinsu a Kano

Daraktan hukumar a jihar shi ne Hassan Mamman Joda wanda ya ke rike da kujerar tun bayan karbo ta daga Kano a shekarar 2012.

Malam Yahaya Yakub Adam, mataimakin daraktan Hisbah a jihar ya fadawa Legit Hausa yadda suke gudanar da ayyukansu.

"Abubuwan da muke yi ya sha bamban da wasu saboda mun kasance kamar kungiyar agaji saboda har yanzu ba ma hannun gwamnatin mu muke kula da kanmu.
"Muna bada agaji ga kowa ko da kuwa Kiristoci ne muna taimaka musu idan bukatar hakan ta taso."

- Yahaya Yakub

5. Bauchi

Jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ta na da hukumar Hisbah ke da matukar tasiri a jihar wanda Aminu Balarabe Isa ke jagoranta.

Kokarin jin ta bakin daraktan hukumar a jihar ko wani daga cikin masu fada aji ya ci tura saboda rashin samun damar ganawa da su.

Sauran jihohin da suke da kungiya ko kuma hukumar Hisbah sun hada da Sokoto da Jigawa da Kaduna da sauransu.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya sasanta da Aminu Daurawa, ya koma kwamandan Hisbah gadan-gadan

Abba Kabir ya yi sulhu da Daurawa

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa sun yi sulhu bayan murabus din shugaban hukumar.

Wannan na zuwa ne bayan cece-kuce da ake yi da kiraye-kiraye kan murabus din da ake ganin zai iya dagula al'amura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel