Ta'addanci: Kamar Buhari, Obasanjo Ya Samo Mafita, Ya Fadi Dalilin Matsalar Tsaro

Ta'addanci: Kamar Buhari, Obasanjo Ya Samo Mafita, Ya Fadi Dalilin Matsalar Tsaro

  • Yayin da ake fama da matsalar garkuwa da mutane a Najeriya, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya kawo mafita
  • Obasanjo ya bayyana cewa rashin aikin yi ne babban matsalar da ake samu wanda ya ke jefa mutane cikin ayyukan ta'addanci
  • Tsohon shugaban kasar ya ba da shawarar rungumar harkar noma domin samun kudin shiga da kuma aikin yi a kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya fadi abin da ke kara matsalar garkuwa da mutane a Najeriya.

Obasanjo ya ce rashin aikin yi a tsakanin matasa shi ne babban dalilin ingiza matasa cikin ayyukan ta'addanci.

Kara karanta wannan

Akwai hannun na kusa da Buhari: Omokri ya fallasa wadanda suka kubutar da wakilin Binance

Obasanjo ya fadi hanyar dakile ta'addanci a Najeriya
Olusegun Obasanjo ya ce rashin aikin yi ke kara ayyukan ta'addanci a Najeriya. Hoto: Pius Utomi Ekpei.
Asali: Getty Images

Musabbabin ƙaruwar ta'addanci a Najeriya

Tsohon shugaban ya bayyana haka a wani babban taron kasuwanci a jiya Talata 26 ga watan Maris a Legas, cewar rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tabbas idan muka cimma wannan burin za mu inganta bangaren tsaron Najeriya."
"Matsalar da muke samu na tsaro mata ne da matasa wadanda ba su da aikin yi, idan muka ba su aiki ayyukan ta'addanci za su ragu sosai."

- Olusegun Obasanjo

Wace hanya za ta dakile ta'addanci?

Obasanjo ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi imani da harkokin noma inda ya ce dole a mai da noma mafi muhimmanci a Najeriya.

Ya ce inganta harkokin noma ne kadai zai samar da abinci da rage yawan zaman banza da samar da kudin shiga, cewar Daily Post.

"Wani abokina ya taba ce min ni nahaukaci ne, na ce me yake nufi? Sai ya ce idan ba mahaukaci ba babu wanda zai shiga harkar noma."

Kara karanta wannan

An sake shiga jimami bayan fitaccen jarumin fina-finai ya kwanta dama

"Tabbas ni mahaukaci ne kan harkar noma, idan dai a kan noma ne ka kira ni da wannan suna tabbas zan amsa."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya ba Tinubu shawara mai kyau

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yadda zai kawo karshen matsalar tattalin arziki.

Obasanjo ya shawarci Tinubu ya nemi taimakon kasar Zimbabwe tun da sun taba shiga matsalar kuma sun wanye lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel