Obasanjo Ya Fadi Hanyar da Za a Bi a Gyara Najeriya Cikin Sauki

Obasanjo Ya Fadi Hanyar da Za a Bi a Gyara Najeriya Cikin Sauki

  • Olusegun Obasanjo wanda ya shugabanci Najeriya a lokacin mulkin soja da na farar hula, ya yi kira ga al'umma ƙasar nan
  • Tsohon shugaban ƙasan ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su yanke ƙauna da ƙasar nan duk da halin wuyar da ake ciki
  • Ya kuma buƙaci shugabanni da su yi amfani da damar da suka samu ta jagorantar jama'a kan hanyar da ta dace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su yanke ƙauna da ƙasar nan.

Obasanjo ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara ga Gwamna Godwin Obaseki, na jihar Edo a gidan gwamnati da ke birnin Benin, babban birnin jihar, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Kungiya ta yi magana kan zargin da ake yi wa ministsn Tinubu na ba 'yan bindiga tallafin abinci

Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya
Obasanjo ya bukaci 'yan Najeriya kada su yanke kauna da kasar nan Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

Da yake yaba wa gwamnan bisa irin tarbar da ya yi masa, tsohon shugaban ƙasan ya buƙaci shugabanni da su kasance masu sadaukarwa da rashin son kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Obasanjo ya bada?

Ya yi nuni da cewa halin da ake ciki a ƙasar nan yana da matuƙar wahala, amma za a iya sauya shi idan akwai kyakkyawar niyya.

Ya yi kira da a riƙa tunatar da masu madafun iko su yi amfani da damar da suka samu ta jagorantar al'umma yadda ya dace.

A kalamansa:

"Halin da ake ciki a Najeriya yana da wahala, amma babu wani yanayi mara kyau da ba zai iya yin kyau ba. Tambayar ita ce, yaushe kuma ta yaya?
"Abin da ya kamata mu ce ga waɗanda suka samu dama a yanzu shi ne su yi iya ƙoƙarinsu. Lallai wata dama ce gare ku ku tafiyar da al'amuran ƙasarku da kuma kula da al'ummar ku. Wannan dama ce.

Kara karanta wannan

Jigo a PDP ya ba Tinubu shawara kan hanyar da zai bi domin faranta ran 'yan Najeriya

"Bai kamata ya zama ni ba sai mu, ba nawa ba sai namu, ba gobe na ba amma gobenmu, kuma ba lokacina ba amma dukkan lokuta har da ƴan baya masu zuwa.
"Wannan shi ne abin da ci gaba mai ɗorewa yake nufi. Ba ku ci yau ba kuma ba ku tunanin ƴan baya da suke zuwa waɗanda su ma za su ci, haka abun yake."

Obasanjo ya faɗi illar da ake yi wa Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi fallasa kan ɓarnar da ake tafkawa a ɓangaren man fetur na ƙasar nan.

Obasanjo ya bayyana cewa sama da kaso 80% na man fetur ɗin da ake samarwa a ƙasar nan, a hannun ɓarayi yake tafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel