Wasu 'yan tsibbu da suka dade suna damfarar mutane sun shiga hannun hukuma
Hukumar 'Yan sandan jihar Enugu tayi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi 'yan damfara ne wanda suka dade cutar mutane da cewa zasu iya magance musu duk matsaloli rayuwa da suke fama da shi.
Wanda ake zargin, Akin Ogunsemi da Shina Fatola 'yan asalin garin Ijebu Igbo ne da ke jihar Ogun.
Kakakin hukumar 'Yan sanda na jihar Enugu, Mr. Ebere Amaraizu ya bayar da wannan sanarwan a jiya Juma'a inda ya kara da cewa an cafke Ogunsemi da Fatola ne a Ukwuoji a Emene na jihar Enugu a ranar 1 ga watan Mayu.
'Yan sanda na musamman masu yaki da 'yan kungiyar asiri sun ce anyi nasarar kama mutane biyun ne sakamakon wasu bayannan sirri da hukumar ta samu.
KU KARANTA: A karo na farko, za'a gina wa Kiristoci coci a kasar Saudiyya
Amaraizu, yace mutanen biyu sun kware wajen damfarar mutane inda suke cewa su masu magani ne kuma suna karbewa mutane kudaden su da dukiyoyi.
A yayinda aka kama su, an same su da kudaden kasashen waje na bogi, laya da guri da wasu kayayakin da ake tsamani na tsibbu ne.
A wata cigaban kuma, hukumar Yan sandan tayi nasarar kama wasu dalibai 25 a yankin kudu maso gabashin Najeriya yayin da suke gudanar da wani taron kungiyar asiri.
An kama su ne a dajin Obeagu da ke Amechi, Awkunawaw da ke jihar Enugu, ana zargin matasan mambobin wata kungiyar asiri ne da ke kira Black Axe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng