Sakamakon damfarar N5.6m: Wani malamin tsubbu zai shafe shekaru 97 a kurkuku

Sakamakon damfarar N5.6m: Wani malamin tsubbu zai shafe shekaru 97 a kurkuku

- Kotu ta yankewa wani malamin tsubbu adadin shekaru 97 a gidan yari sakamakon kamashi da laifin damfarar wani mutum N5.6m

- Kotun ta yankewa Clement Joshep wannan hukuncin bayan samunsa da aikata laifuka bakwai da suka shafi damfara

- Haka zalika, kotun ta umurci Mr Joshep da ya mayar da N5.6 ga Mr Bola Akibola, wanda hukumar EFCC ta shigar da karar a madadinsa

Mai shari'a Angela Otaluka ta babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, a ranar Laraba ta yankewa wani malamin tsubbu mai shekaru 43, Clement Joshep, adadin shekaru 97 a gidan yari sakamakon kamashi da laifin damfarar wani mutum N5.6m.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da Joseph, wanda aka fi sani da 'Dr Omale', gaban kotun bisa zarginsa da aikata laifuka bakwai da suka shafi karbar kudi ta hanyar yin karya.

Da ta ke yanke hukunci kan shari'ar, Mrs Otaluka ta bayyana cewa bangaren da ke shigar da karar sun gabatar da hujjojinsu akan wanda ake karar kuma kotu ta samu wanda ake karar da aikata laifuka bakwai.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Gobara ta tashi a ofishin cibiyar NPC da ke Abuja

Sakamakon damfarar N5.6m: Wani malamin tsubbu zai shafe shekaru 97 a kurkuku
Sakamakon damfarar N5.6m: Wani malamin tsubbu zai shafe shekaru 97 a kurkuku
Asali: Depositphotos

Da wannan ne ta yanke masa hukuncin shekaru bakwai akan laifi daya ba tare da biyan kudin fansa ba da kuma yanke masa hukuncin shekaru 15 a kan kowanne laifi cikin laifuka na 2 zuwa na bakwai ba tare da tara ba.

Sai dai, mai shari'ar ta bayar da umurnin cewa wanda ake karar zai yi zaman wakafinne a jere, hade da shekaru biyun da ya riga ya kwashe a gidan wakafin kafin yanke masa wannan hukunci.

Haka zalika, Mrs Otaluka ta baiwa wanda aka yankewa hukuncin umurnin mayar da N5.6 ga Mr Bola Akibola, wanda hukumar EFCC ta shigar da karar a madadinsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel