CAC: Hukumar Kula da Kamfanoni Ta Najeriya Na Daukar Aiki? Gaskiya Ta Bayyana

CAC: Hukumar Kula da Kamfanoni Ta Najeriya Na Daukar Aiki? Gaskiya Ta Bayyana

  • Hukumar da ke kula da harkokin kamfanoni (CAC) ta karyata rahoton da ke yawo a soshiyal midiya na cewa ta fara daukar aiki
  • A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, hukumar CAC ta gargadi jama'a kan su yi hattara da 'yan damfara
  • CAC, a matsayinta na hukuma mai bin doka da oda ta ce ba za ta taba fara daukar ma'aikata ba tare da bin dokar kasa ta FCP ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar da ke kula da harkokin kamfanoni (CAC), ta ce ba ta daukar ma’aikata a halin yanzu, inda ta shawarci ‘yan Najeriya da su yi hattara da 'yan damfara.

Kara karanta wannan

Hukumar JAMB ta dauki mataki kan wasu jami'anta da suka ci zarafin daliba mai hijabi

Hukumar CAC ta yi karin haske kan batun daukar ma'aikata a halin yanzu
Hukumar CAC ta gargadi 'yan Najeriya da su yi hattara da 'yan damfara. Hoto: @cacnigeria1
Asali: Twitter

Hukumar ta CAC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu.

Magaji ya magance matsalolin CAC

Sanarwar ta ce an jawo hankalin hukumar kan wasu rahotannin karya da ake yadawa a soshiyal midiya da ke cewa tana daukar ma’aikata, wanda ya sabawa dokar kasa ta FCP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar, shugaban hukumar CAC, Hussaini Magaji, bayan hawansa mulki a ranar 16 ga Oktoba, 2023, ya fuskanci kalubale masu tarin yawa.

Ta ce wadannan kalubalen sun hada da tarin ma'aikatan da ba a yi masu karin girma ba zuwa wasu batutuwan da suka shafi walwalar ma'aikata.

Hukumar CAC na bin doka da oda?

Sanarwar ta ce domin inganta jin dadin ma’aikatan CAC, Mista Magaji ya warware matsalolin da suka shafi karin girma a shekarar 2022 kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta fara ƙera motoci gadan-gadan, gwamnatin tarayya ta yi bayani

“A yayin gudanar da aikin, an yi wa ma'aikata da dama karin girma zuwa jami’an zartarwa da wadanda ba na zartarwa ba kamar yadda doka ta tanada.

- A cewar sanarwar.

Sanarwar ta bayyana cewa, CAC, a matsayinta na hukuma mai bin doka da oda, ba za ta taba fara daukar ma'aikata ba tare da amincewar hukumomin da suka dace ba.

CBN zai daidaita farashin Naira

A wani labarin, babban bankin Najeriya (CBN) ya jaddada kudurinsa na daidaita farashin Naira a kasuwar hada-hadar kudade ta duniya.

Legit Hausa ta rahoto gwamnan bankin, Yemi Cardoso wanda ya bayyana hakan ya kuma ce Najeriya ta samu karin masu zuba jari daga kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.