Kwamishinoni Sun Ba Hammata Iska a Taron Karbar Sababbin Tuba Daga PDP Zuwa APC

Kwamishinoni Sun Ba Hammata Iska a Taron Karbar Sababbin Tuba Daga PDP Zuwa APC

  • Yayin da ake bikin karbar sabbin tuba daga jam'iyyar PDP zuwa APC, wasu kwamishinoni a jihar Ebonyi sun gwabza da juna
  • Kwamishinan muhalli, Victor Chukwu da na yada labarai, Jude Okpor sun gwabza yayin da ake tsaka da taron siyasa a jihar
  • Lamarin ya faru ne a garin Ebiaji da ke karamar hukumar Ezza ta Arewa yayin da wasu jiga-jigan PDP ke sauya sheka zuwa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ebonyi - An yi abin kunya yayin da kwamishinoni a jihar Ebonyi suka kaure da fada yayin taron siyasa.

Kwamishinonin guda biyu Jude Okpor da Victor Chukwu sun kaure ne yayin da ake taron karbar jiga-jigan jami'yyar PDP zuwa APC mai mulkin jihar.

Kara karanta wannan

Neja: An shiga fargaba bayan 'yan bindiga sun sake hallaka sojoji tare da sace Kyaftin

Kwamishinoni 2 sun barke da fada ana tsaka da taron siyasa
Wasu kwamishinoni sun ba hamata iska yayin taron siyasa a jihar Ebonyi. Hoto: Francis Nwifuru.
Asali: Twitter

Yaushe kwamishinonin suka gwabza a bainar jama'a?

Lamarin ya faru ne a garin Ebiaji da ke karamar hukumar Ezza ta Arewa yayin da jiga-jigan PDP ke sauya sheka zuwa APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hatsaniyar da ta faru tsakanin kwamishinonin muhalli da yada labarai ta jawo hankulan jiga-jigan jam'iyyar da ke wurin taron.

Wani shaidar gani da ido, Nwite ya fadawa Vanguard cewa kwamishinonin sun manta da girmansu a cikin al'umma inda suka gwabza a tsakaninsu.

Ya ce sai da masu ruwa da tsakin jami'yyar suka shiga tsakani domin dakile matsalar a wurin taron.

Yadda lamarin ya faru a taron siyasa

"Babu wanda ya fadamin, da ido na na gansu suna fada, bansan mene dalilin fadan ba amma wannan shi ne karo na biyar da suke fada."
"A matsayina na shugaban yanki na, wannan abin kunya ne a gare mu, ya faru lokacin karbar jiga-jigan PDP zuwa APC a Ezza ta Arewa."

Kara karanta wannan

"Musulmi ne ko Kirista": APC da PDP sun gwabza kan ainihin addinin gwamna, an kawo hujjoji

"An gwabza kazamar fada kuma ba ta wasa ba, saboda ba a boye ta ke ba."

- Nwite

Gwamna ya kunyata ciyaman cikin jama'a

Kun ji cewa Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya zazzagi wani shugaban karamar hukuma a jihar.

Soludo ya bubbude shugaban, Pascal Aniegbuna a bainar jama'a kan zargin rashin kula da aikinsa a yankin da ya ke jagoranta.

Gwamnan daga bisani ya ba ciyaman din umarni inda ya yi masa barazana kan rasa kujerarsa idan bai dauki mataki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel