Baɗaƙalar N80bn: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana Kan Rikicin Yahaya Bello da EFCC

Baɗaƙalar N80bn: Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana Kan Rikicin Yahaya Bello da EFCC

  • Gwamnatin tarayya ta shawarci tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya miƙa kansa ga hukumar EFCC domin bincike
  • Ministan shari'a kuma Antoni Janar na ƙasa, Lateef Fagbemi, ya ce hukumar EFCC na da ƙarfin ikon gayyatar kowa bisa tanadin doka
  • A cewar lauyan gwamnatin tarayyar, babu wani ɗan Najeriya da ya zama shafaffe da mai wanda ya fi ƙarfin doka ta yi aiki a kansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi kira ga tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi ɗa'a ga doka kuma ya miƙa kansa ga EFCC domin a gudanar bincike.

Antoni Janar na Ƙasa (AGF) kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi, SAN, ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta yi barazanar hada-kai da sojoji domin kamo tsohon gwamnan APC

Yahaya Bello.
FG ta nemi tsohon gwamnan jihar Kogi ya miƙa kansa ga EFCC Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Yadda EFCC ke neman kama Yahaya Bello

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) na neman Yahaya Bello ruwa a jallo kan zargin almundahanar maƙudan kuɗaɗe a lokacin da yana kujerar gwamnan Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Leadership ta ce cikin sa'o'i 24 da suke wuce, jami'an EFCC sun yi yunƙurin kama tsohon gwamnan amma ya kubce masu da taimakon gwamnan Kogi mai ci, Usman Ododo.

Gwamnati na tare da EFCC ko Bello?

Da yake martani kan abin da ya faru, ministan shari'a ya bayyana cewa EFCC na da ƙarfin ikon da za ta gayyaci kowane ɗan Najeriya domin bincike.

Ministan ya kuma bayyana matakin da Gwamna Ahmed Ododo, wanda ya yi amfani da kariyarsa wajen hana cafke Bello ranar Laraba a matsayin abin da bai kamata ba.

A cewar AGF, irin wannan taimakon domin wani ya tsere wa doka illa ce da za ta iya ɓata Najeriya a idanun sauran ƙasashen duniya, a cewar Channels tv.

Kara karanta wannan

"Ɗaurin shekaru 5": EFCC ta ja kunnen gwamnan APC da masu kawo cikas kan Yahaya Bello

Ministan ya jaddada cewa yana tare da bin doka da oda kuma zai yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa ba a tauye hakkin kowane dan Najeriya ba.

Jawabin Minista a kan EFCC v Yahaya Bello

Wani sashin sanarwar ya ce:

"Yanzu dai babu shakka doka ta ba hukumar EFCC ikon gayyatar duk wanda ya kamata duk matsayinsa a yayin gudanar da bincike kan wani lamari.
"Saboda haka, mafi ƙarancin abin da ya kamata mu yi idan an gayyace mu, ba wai mu kawo cikas ga hukumar EFCC ba, mu amsa gayyatarsu cikin mutunci."

- AGF

EFCC ta shirya gurfanar da Yahaya Bello

A wani rahoton kuma hukumar EFCC za ta gurfanar da Yahaya Bello da sauran mutum uku da ake tuhuma a gaban kotun tarayya mai zama a Abuja.

Wannan na zuwa ne yayin da jami'an hukumar suka gamu da cikas a kokarin cafke tsohon gwamnan jihar Kogi a gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel