Dakatar da Ganduje: Jam'iyyar APC Ta Mayar da Martani Kan Hukuncin Babbar Kotun Kano

Dakatar da Ganduje: Jam'iyyar APC Ta Mayar da Martani Kan Hukuncin Babbar Kotun Kano

  • Jam'iyyar APC ta ƙasa ta yi fatali da hukuncin babbar kotun jihar Kano kan dakatar da shugabanta na ƙasa, Abdullahi Ganduje
  • Mai ba APC shawara kan harkokin shari'a, Farfesa Abdulkarim Kana, ya ce za su kai ƙorafi ga NJC domin a tsawatarwa alkalin da ya ba da umarnin
  • Ganduje ya bayyana cewa waɗanda suka dakatar da shi ƴan damfara ba shugabannin jam'iyyar APC da ke gundumarsa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar All Progressives Congress watau APC ya mayar da martani kan hukuncin da babbar kotun jihar Kano ta yanke.

Idan ba ku manta ba, mun kawo maku rahoton cewa kotun ta tabbatar da dakatarwan da aka yi wa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Daga karshe an bayyana wadanda suka 'kitsa' shirin

Shugaban APC na kasa, Ganduje.
Dakatar da Ganduje: APC ta yi fatali da umarnin babbar kotun jihar Kano Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Ganduje: APC ta mayar da martani

Yayin mayar da martani, kwamitin NWC na APC ya bayyana umarnin kotu a matsayin mara amfani wanda ba zai yi aiki ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NWC ta yi fatali da umarnin kotun ne yayin da Ganduje ya karɓi bakuncin shugabannin APC na gundumar Ganduje da ke ƙarar hukumar Dawakin Tofa a Kano.

Shugabannin sun ziyarci babbar sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuje ne domin jaddada mubaya'arsu da kwarin guiwa ga Ganduje, The Nation ta tattaro wannan.

Da yake jawabi ga shugabannin jam'iyyar APC na gundumarsa, Ganduje ya ce wadanda aka ce sun dakatar da shi ’yan damfara ne kawai.

Wani mataki APC ta ɗauka?

Da yake nasa jawabin, mai ba jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Farfesa Abdulkarim Kana, ya ce umurnin babbar kotun Kano ba zai yi aiki ba domin an same shi ta hanyar zamba.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan dakatarwar da aka yi wa Ganduje daga jam'iyyar APC

Ya ce shugabannin gundumar Ganduje za su kai ƙorafi ga hukumar shari’a ta kasa NJC domin ta tsawatarwa alkalin babbar kotun jihar Kano wanda ya ba da wannan umarni.

Zanga-zanga ta ɓarke a hedkwatar PDP

A wani rahoton kuma 'yan PDP sun ɓarke da zanga-zanga, sun mamaye babbar hedkwatar jam'iyya ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Masu zanga-zangar sun jaddada goyon bayansu ga muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel