Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Umarnin Kotu, Ta Faɗi Mutanen da Suka Dakatar da Ganduje

Jam'iyyar APC Ta Yi Magana Kan Umarnin Kotu, Ta Faɗi Mutanen da Suka Dakatar da Ganduje

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta ce ta samu labarin umarnin kotu na dakatar da shugabanta na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje
  • Mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a, Abdulkarim Kana, ya ce amma har yanzun umarnin bai zo hannun APC ba tukuna
  • Farfesa Kana ya kuma bayyana cewa waɗanda suka jagoranci dakatar da Ganduje a gundumarsa ba mambobin jam'iyyar APC ba ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa har yanzun ba a kawo mata takardar umarnin kotu na dakatar da shugaban jam'iyyar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ba.

Mai bai APC shawara kan harkokin shari'a, Abdulkarim Kana, ne ya bayyana haka a babbar sakatariya da ke Abuja, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kotu ta bada umurni dabam kan dakatar da Ganduje

Tsohon gwamnan Kano, Ganduje.
APC ta ce ba a kawo mata takardar umarnin kotu ba Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Yadda aka dakatar da Ganduje a APC

A ranar 15 ga watan Afrilu, wasu da suka kira kansu shugabannin APC a gundumar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Kano suka dakatar da Ganduje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jim kaɗan bayan haka, kwamitin gudanarwa na APC ta jihar Kano ya soke dakatarwan tare da hukunta shugabannin jam'iyyar na gunduma.

Sai dai wata babbar kotun jihar Kano ta tabbatar da dakatar da Ganduje, tsohon gwamnan jihar a wata kara da Ibrahim Sa’ad ya shigar a madadin shugabannin gundumar.

Ganduje: APC ta faɗi masu hannu a batun

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Laraba, Kana ya jaddada cewa wadanda ke da hannu a dakatar da Ganduje ba mambobin jam’iyyar APC ba ne.

“Mun ji labarin umarnin kotu da yammacin yau, amma ba mu ga takardar ba har yanzu. Mutanen da ke da hannu a wannan lamarin ba ’yan APC ba ne.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Daga karshe an bayyana wadanda suka 'kitsa' shirin

"Ba mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC a Kano ba ne, ba mu sansu ba kwata-kwata. Tuni APC ta shigar da ƙorafi gaban sufetan ƴan sanda na ƙasa."

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tun da farko shugabannin APC na Dawakin Tofa sun ziyarci Ganduje a hedkwatar APC ta ƙasa domin nuna damuwarsu kan abin da ya faru.

Babu shirin canja shugabancin PDP

A wani rahoton na daban Gwamnonin jam'iyyar PDP sun musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ana shirin canja shugaban jam'iyya, Umar Damagum.

Gwamna Bala Mohammed na Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin ya ce babu batun sauya shugabanci a shirin taron jam'iyyar adawar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel