Badakalar N80bn: Yahaya Bello Na Fuskantar Sabuwar Matsala, EFCC Ta Sake Kai Shi Kotu

Badakalar N80bn: Yahaya Bello Na Fuskantar Sabuwar Matsala, EFCC Ta Sake Kai Shi Kotu

  • Hukumar yaki da masu yi wa dukiyar al'umma zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya a Abuja
  • EFCC na tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi da aikata wasu laifuffuka 17 da suka hada da karkatar da N80bn da kuma yin safararsu
  • Wannan na daga cikin kwaskwarimar da hukumar ta yi kan karar da data shigar da dan uwan Bello da wasu mutane kan laifin safarar kudi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Adoza Bello a gaban babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja.

Hukumar na tuhumar Yahaya Bello da ɗan uwansa Ali Bello da wani Dauda Sulaiman da Abdulsalam Hudu da aikata laifuffuka na karkatar da Naira biliyan 80 da safararsu.

Kara karanta wannan

Buga takardun bogi: Kotu ta dauki mataki kan tsohon shugaban bankin NIRSAL, Abdulhameed

EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu
EFCC na tuhumar Yahaya Bello da yin safarar N80bn. Hoto: @YahayaBello, @officialEFCC
Asali: Twitter

Yadda EFCC ta saka Bello a shari'ar

Wannan wata kwaskwarima ce hukumar ta yi kan karar da ta shigar da mutanen a baya, na tuhumarsu da laifuffuka 17 da suka shafi safarar kudi, cin amana da satar kudin al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ce ta bayyana hakan a shafinta X, inda ta ce lauyanta, Rotimi Oyedepo, SAN, ya sanar da kotun cewa sun yi wa karar kwaskwarima domin saka Yahaya Bello a cikin wadanda take tuhuma.

Oyedepo ya roki kotun da ta karbi wannan gyara nata tare da karanta shi ga wadanda take karar, bukatar da A.M Aliyu, SAN, da Olusegun Joolawo, SAN, lauyoyin wadanda ake kara suka nuna jayayya a kai.

Abin da tuhumar EFCC ta kunsa

Sai dai alkalin kotun, Mai shari'a James Omotosho ya amince da bukatar EFCC, na hada Yahaya Bello a cikin wadanda ake tuhuma da laifukan 17.

Kara karanta wannan

Hukumar shige da fice ta magantu kan umarnin Tinubu na bude iyakar Najeriya da Nijar

Tuhume tuhumen da EFCC ta gabatar wa kotun sun hada da:

"Cewa Ali Bello, Dauda Suleiman, Yahaya Adoza Bello da Abdulsalam Hudu, a watan Satumba 2015 a Abuja, sun yi safarar N80,246,089.88.
"Safarar wadannan kudi na tattare da laifuffukan aikata zamba, karkatar da kudi, wanda ya sabawa sashe na 18(b) kuma yake da hukunci a sashe na 15(3) a dokar haramta safarar kudi ta 2011."

Mai shari'a Omotosho ya dauki mataki

Yayin da Yahaya Bello da Hudu suka ki bayyana a zaman kotun, Ali Bello da Suleiman wadanda suka halarci zaman sun musanta aikata dukkan laifuffukan da aka karanta masu.

EFCC ta yi zargin cewa wadanda take kara sun yi amfani da kudin wajen sayen kadarori a Abuja, ciki har da wani gida da ke a unguwar Danube, Maitama, wanda aka saya a kan N950m.

Mai shari'a Omotosho ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 28 ga watan Maris, tare da neman EFCC ta gabatar da hujjojinta.

Kara karanta wannan

An samu bullar cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi 7 a Arewacin Najeriya

Karanta sanarwar a nan:

Kotu ta garkame Ali Bello

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin garkame ali Bello, dan uwan tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan da hukumar EFCC ta gurfanar da Bello akan zarginsa da satar akalla Naira biliyan uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel