Jerin Lokuta 11 da 'Yan Ta'adda Suka Shiga Makaranta Tare da Sace Dalibai a Najeriya

Jerin Lokuta 11 da 'Yan Ta'adda Suka Shiga Makaranta Tare da Sace Dalibai a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

A lokuta da dama ƴan ta'adda sun sha kutsawa cikin makarantu suna yin awon gaba da ɗalibai a Najeriya.

Satar ɗaliban ta jefa shakku kan kare lafiya da tsaron ƴan makaranta waɗanda suke zuwa neman ilmi a makarantun.

satar dalibai a Najeriya
Sace dalibai na jefa iyayensu cikin tashin hankali Hoto: Umar Audu Marte
Asali: Getty Images

Wasu daga cikin ɗaliban bayan an sace su suna kuɓuta, yayin da wasu kuma suke haɗuwa da ajalinsu a hannun ƴan ta'addan.

Lokutan da aka sace ɗalibai a Najeriya

Jaridar TheCable ta jero lokuta 11 da ƴan ta'adda suka shiga makarantu tare da yin awon gaba da ɗalibai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

FGC Buni Yadi, jihar Yobe

A ranar 25 ga watan Fabrairun 2014 ƴan ta'addan Boko Haram suka sace ɗalibai maza 58 na kwalejin gwamnatin tarayya da ke Buni Yadi a jihar Yobe.

Kara karanta wannan

Kano: Ana fargabar mutum 45 sun rasa rayukansu sakamakon barkewar sabuwar cuta

Ƴan ta'addan sun hallaka dukkanin ɗaliban bayan sace su. Shekara uku bayan kai harin an cafke wanda ya jagoranci harin, Abdulkadir Abubakar, wanda har yanzu yake tsare a hannun sojoji.

Sakandiren Chibok, jihar Borno

A ranar 14 ga watan Afirilun 2014 ƴan ta'addan Boko Haram suka dira a makarantar sakandiren kwana ta mata da ke Chibok a jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun yi awon gaba da ɗalibai 276 zuwa cikin daji. Yayin da yawa daga cikin ƴan matan waɗanda yanzu sun zama manya sun kuɓuta, har yanzu akwai waɗanda ke tsare a hannun ƴan ta'addan.

Makarantar sakandiren Dapchi, jihar Yobe

Ƴan ta'addan Boko Haram a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018, sun sace ɗalibai masu yawa a kwalejin gwamnatin tarayya ta mata da ke Dapchi a jihar Yobe.

Waɗanda aka sace sun haɗa da ɗalibai 111 na makarantar da wasu ɗalibai biyu na wata makarantar firamare.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi sabuwar ta'asa ta kashe mutane a jihar Kaduna

Biyar daga cikin matan sun rasu a hannun ƴan ta'addan yayin aka sako sauran face guda ɗaya, Leah Sharibu, wacce har yanzu take tsare a hannunsu saboda ta ƙi musulunta.

Makarantar sakandiren Kankara, jihar Katsina

A ranar 11 ga watan Disamban 2020 ƴan bindiga suka dira makarantar sakandiren kwana ta maza da ke Kankara a jihar Katsina, inda suka sace ɗalibai 300.

An sako ɗaliban kwanaki shida bayan sace su sakamakon ƙoƙarin da gwamnatin jihar ta yi.

Makarantar Kagara, jihar Neja

Ƴan bindiga sun kai hari a kwalejin kimiyya da ke Kagara a jihar Neja a ranar 17 ga watan Fabrairun 2021, inda suka sace mutum 41 da suka haɗa da malamai, ɗalibai da iyalan malaman.

Daga baya an sako su bayan an tattauna da ƴan bindigan da suka sace su.

Makarantar sakandiren Jangebe, jihar Zamfara

A ranar 26 ga watan Fabrairun 2021 ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata guda 300 na makarantar sakandiren gwamnati da ke Jangebe a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai ƙazamin farmaki hedkwatar ƙaramar hukuma, sun tafka ɓarna

Cikin nasara gwamnatin jihar ta sanar da ceto su ƴan kwanaki kaɗan bayan an sace su.

Makarantar Islamiyya da ke Tegina, jihar Neja

Sama da ɗalibai 150 na makarantar Islamiyya ta Salihu Tanko da ke ƙaramar hukumar Rafi ƴan bindiga suka yi awon gaba da su a ranar 30 ga watan Mayun 2021.

Wasu daga cikin ɗaliban sun rasu a hannun ƴan bindigan, yayin da aka ceto ragowar bayan wasu watanni.

Makarantar Birnin-Yauri, jihar Kebbi

A ranar 17 ga watan Yunin 2021, ɗalibai masu yawa da malamansu ƴan bindiga sama da 100 suka sace a kwalejin gwamnatin tarayya da ke Birnin-Yauri a jihar Kebbi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Ƴan bindigan sun kai farmaki a makarantar kwanan ne a kan babura inda suka hallaka wani ɗan sanda da raunata wasu ɗaliban kafin su sace ɗalibai da malamai waɗanda ba a san yawansu ba.

Dakarun sojoji sun ceto wasu daga cikinsu yayin da wasu aka sako su bayan an biya kuɗin fansa.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan matan Chibok suka dawo da yara 34 bayan Boko Haram sun sako su

Sauran ɗaliban kuma sun shaƙi iskar ƴanci ne bayan sun kwashe watanni a tsare.

Makarantar Bethel Baptist, jihar Kaduna

A cikin tsakar daren ranar 5 ga watan Yulin 2021 ƴan bindiga suka sace ɗalibai da malamansu a makarantar Bethel Baptis da ke Damishi, a jihar Kaduna. 

Sace ɗaliban ya jawo tayar da jijiyar wuya a jihar, inda ya sanya aka shiga damuwa kan tsaron ɗaliban da ke makarantun kwana a Najeriya.

Makarantar firamare, jihar Nasarawa

Ƴan bindiga sun sace ɗalibai na makarantar firamare da ke jihar Nasarawa bayan sun kai hari a ranar 20 ga watan Janairun 2023.

Ƴan bindigan sun kai farmaki a makarantar ne da misalin ƙarfe 7:00 na safe inda suka sace ɗalibai shida.

An ceto biyu daga cikinsu kwana ɗaya bayan sace su yayin da sauran suka kwashe kwanaki 14 a tsare kafin a ceto su.

Makarantar Apostolic Faith, jihar Ekiti

A ranar 30 ga watan Janairun 2024 ƴan bindiga sun farmaki motar makarantar sakandare ta Apostolic Faith a jihar Ekiti inda suka sace ɗalibai masu yawa tare da malami ɗaya da direban motar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta sha alwashin ceto ragowar 'yan matan Chibok da ke hannun Boko Haram

Kwanaki huɗu bayan sace su an ceto ɗaliban tare da malaminsu yayin da aka samu gawar direban.

Makarantar Kuriga, jihar Kaduna

A ranar 7 ga watan Maris 2024 ƴan bindiga sun dira a makarantar sakandiren gwamnati da ke Kuriga a jihar Kaduna inda suka sace ɗalibai 287 tare da hallaka wani ɗan banga mutum ɗaya.

Gwamnan jihar, Uba Sani, ya sanar da ceto su bayan wasu ƴan makonni amma bai bayyana cewa an biya ko ba a biya kuɗin fansa ba kafin a ceto su.

Makarantar Tsangaya, jihar Sokoto

A ranar 9 ga watan Maris 2024, ƴan bindiga suka kai farmaki a makarantar Tsangaya da ke Gidan Bakuso a ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto inda suka sace almajirai 15.

Dakarun sojoji sun ceto ɗaliban bayan sun kwashe kwanaki 14 a tsare a hannun ƴan bindigan.

Ƴan bindiga sun saki ɗalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaliban jami'ar tarraya ta Wukari da ke jihar Taraba sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe aƙalla mako biyu a hannun ƴan bindiga.

Ƴan bindigan sun saki ɗaliban ne bayan kowannensu ya biya wani ƙayyadadden adadi na kuɗin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng