El-Rufai Ya Fallasa Gwamnatin Tarayya, Har Yanzu Tinubu Na Biyan Tallafin Fetur

El-Rufai Ya Fallasa Gwamnatin Tarayya, Har Yanzu Tinubu Na Biyan Tallafin Fetur

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce har yanzu gwamnatin Bola Tinubu tana biyan tallafin man fetur
  • Ya yi nuni da cewa gwamnati ta ga cewa duk wani shiri na rage radadin janye tallafin ya gaza yin tasiri ya sa aka dawo da biyan tallafin
  • Sai dai El-Rufai, wanda ya ce yana goyon bayan manufar janye tallafin, ya ce dole ne gwamnati ta yi gyare-gyaren da suka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Maiduguri, jihar Borno - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ce tallafin man fetur ya dawo, amma yawancin ‘yan Najeriya ba su san haka ba.

Da yake amsa tambayar manema labarai a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, a ranar Litinin, El-Rufai ya ce gwamnatin tarayya tana biyan kudin tallafi fiye da a baya.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Malam El-Rufa'i ya bayyana babbar matsala 1 tak da ta addabi Najeriya

Mlam Nasir El-Rufai ya yi magana kan biyan tallafin man fetur a Najeriya
El-Rufai ya ce kudin tallafin mai da Najeriya ke biya yanzu ya nunka na baya. Hoto: @elrufai, @officialABAT
Asali: Twitter

Ya yi nuni da cewa gwamnati ta ga cewa duk wani shiri na rage radadin janye tallafin ya gaza yin tasiri, wannan ya sa dole ta dawo da biyan tallafin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa na farko, shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana janye tallafin fetur, yana mai cewa babu wani alfanu a biyan talafin.

Janye tallafin fetur ya gamu da cikas?

Sai dai El-Rufai, wanda ya ce yana goyon bayan manufar janye tallafin, ya ce dole ne gwamnati ta yi gyare-gyaren da suka dace.

“Janye tallafin man fetur wani kudiri ne da shugaban kasa ya aiwatar, kuma kudiri ne mai kyau. A koyaushe ina goyon bayan janye tallafin mai.
“Amma a yayin aiwatarwa kamar yadda kuke gani gwamnati ta fahimci cewa dole ne a dawo da tallafin kuma a halin yanzu, muna biyan makudan kudade fiye da a baya."

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa muka gayyaci Nasir El-Rufai zuwa Borno Inji Gwamnatin Zulum

Ya za a gane ana biyan tallafin fetur?

Jaridar Vanguard ta rahoto El-Rufai ya ce mutane da yawa ba su san cewa gwamnati ta dawo da biyan tallafin man fetur ba.

"“Amma idan suna son sanin ko ana biyan tallafi ko ba a biya, sai su kwatanta farashin man fetur da dizal domin man fetur ya fi dizal tsada amma man dizal yana kan naira dubu daya yayin da man fetur ke kan N600 kan kowace lita.
“Don haka har yanzu muna biyan tallafin man fetur saboda gwamnati ta fahimci akwai kura-kurai a yadda ta janye tallafin man da farko, dole ne a yi wasu 'yan gyare-gyare."

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya ziyarci Maiduguri

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya ziyarci Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A yayin ziyarar ne El-Rufai ya gana da Gwamna Babagana Umara Zulum yayin da ya shirya gudanar da jawabi a wani taron karawa juna suna da gwamnatin jihar ta shirya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel