Tsohon Gwamna, Malam El-Rufa'i Ya Bayyana Babbar Matsala 1 Tak da Ta Addabi Najeriya

Tsohon Gwamna, Malam El-Rufa'i Ya Bayyana Babbar Matsala 1 Tak da Ta Addabi Najeriya

  • Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya ce yunwa, cire tallafin mai da hauhawar farashin canji ba su bane matsalar Najeriya
  • A wurin taron ƙara wa juna sani a Borno, tsohon gwamnan ya ce gazawar shugabanci ne asalin matsalar da ta damu ƙasar nan
  • Ya kuma yabawa Gwamna Babagana Umaru Zulum bisa yadda ya ga jihar Borno ta sauya duk da matsalar ƴan tada ƙayar baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya ce shugabanci shi ne babbar matsalar Najeriya.

El-Rufai ya bayyana haka ne a jawabinsa a wurin taron karawa juna ilimi na manyan jami’an gwamnatin jihar Borno wanda ya gudana ranar Litinin, 15 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

"Akwai damuwa" Gwamna Sule ya jero ƙananan hukumomi 8 da ke cikin babbar matsala

Malam Nasiru El-Rufai.
Gazawar shugabanci ne babbar matsalar Najeriya in ji El-Rufai Hoto: Nasiru El-Rufai
Asali: Facebook

Taron wanda aka yi wa taken, "Inganta kwarewar jami'an gwamnati wajen aiwatar da manufofi da sarrafa albarkatu," ya gudana ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mallam El-Rufai, babban baƙo mai jawabi a taron bitar, yace ya ziyarci jihar Kaduna sau biyar ne kawai tun bayan sauka daga mulki kusan shekara daya da ta wuce.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, tsohon gwamnan ya ce ya yi haka ne saboda ba ya son sukar shugabanni, na yanzu ko waɗanda suka shuɗe.

Asalin matsalar Najeriya

"Abin da muka rasa shi ne jagoranci na gari, babban abin da ke kawo kyakkyawan shugabanci. Wajibi kowane shugaba ya zakulo mutane masu gaskiya domin sauke nauyin da aka ɗora masa.
"Muna iya hangen cewa matsala ɗaya ce ta zame wa Najeriya ƙarfen ƙafa, ba rashin abinci, yunwa, hauhawar farashin canji ko cire tallafin mai bane, matsalar ita ce gazawar shugabanci.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya fallasa gwamnatin tarayya, har yanzu Tinubu na biyan tallafin fetur

- Malam El-Rufai.

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa duk kirki da nagartar shugaba ba zai yi tasiri ba matuƙar bai jawo mutanen arziƙi sun kewaye shi a gwamnati ba.

El-Rufai ya ce ya ji dadin abubuwan da ya gani a Maiduguri da wasu sassan Borno, inda ya ce wuraren sun yi kyau duk da rikicin Boko Haram da aka kwashe sama da shekaru goma ana yi.

El-Rufai ya magantu kan rikicin Kaduna

A wani rahoton kuma Mallam Nasir El-Rufai ya mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa a jihar Ƙaduna karkashin mulkin Uba Sani.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sau biyar kaɗai ya je Kaduna tun bayan sauka mulki saboda ba ya son tsoma baƙi a gwamnati mai ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel