Iftila'i: Mummunar Gobara ta Shafe Kasuwar Boda dake Gaya

Iftila'i: Mummunar Gobara ta Shafe Kasuwar Boda dake Gaya

  • Iftila'in gobara ta shafe baki daya kasuwar Boda dake garin Gaya a karamar hukumar Gaya dake jihar Kano da tsakar daren Asabar
  • Wadanda suka rasa dukiyoyinsu sun ce ba su tsira da komai ba sai suturun jikinsu, amma ba a samu rahoton rasa rai ba
  • Hukumar kashe gobara ta Kano ta bakin jami'in hulda da jama'arta, Saminu Yusuf Abdllahi ya tabbatar da afkuwar gobarar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar wata mummunar gobara kasuwar Boda dake kauyen Fan'idau a garin Gaya dake jihar Kano.

Kara karanta wannan

An sake kai harin da ya yi sanadiyyar kashe mutane 10 a jihar Plateau, jama'a sun shiga firgici

Gobarar ta tashi ne da tsakar dare wayewar Lahadi kamar yadda Legit Hausa ta samu rahoto.

Gobarar ta shafe kasuwar Boda dake garin Gaya
'Yan kasuwar sun ce ba su tsira da komai ba Hoto: Nura Zafi DanJarida Gaya
Asali: Facebook

Abdullahi Tseda Sarkin Kasuwar Boda ya ce yana cikin baƙin cikin da bai taɓa shiga irinsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Ni wannan abin hankalina ya tashi oba fiye da yadda duk mutum yake tunani. Saboda Allah Ya sani ni wannan guri na fi kowa jin baƙin cikin wannan abu, saboda bala'in da ya faru a wannan wuri."

Ƴan kasuwar sun nemi daukin gwamnati

A'isha Tukur, guda daga waɗanda ke sayar da abinci a kasuwar ta ce suna kwance da misalin karfe 3. 15 na dare kawai sai suka ga wutar ta tashi.

A kalamanta:

"Wallahi ba abinda ya tsira, kowacce daga ita sai ɗan kayan jikinta ta samu, amma komai ga shi nan. Allah Ya aiko mana da iftila'i, amma Allah Ya canza mana da abinda ya fi alkhairi."

Kara karanta wannan

Fusatattun Yarbawa na son a raba Najeriya, sun farmaki sakateriyar gwamnati a Oyo

"Ko tsinke ba mu tsira da shi ba."

Abdullahi Adamu, shi ne Mai Unguwar yankin kuma wakilin Dagaci ya ce suna bukatar agajin gaggawa daga bangaren gwamnatoci.

Hukumar gobara ta tabbatar da iftila'in

Saminu Yusuf Abdullahi, jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano ya tabbatar da afkuwar gobarar.

Ya shaidawa Legit Hausa cewa:

"Motar mu tana wajen gyara a nan Kano, ina jin shi yasa ba su sanar da ofishinmu ba."

Gobara ta lakume miliyan 80 a Kano

Mummunar gobara ta lakume kimanin naira miliyan 80 a Gezawa dake jihar Kano, ba a samu asarar rai ko daya ba.

Hukumar gobara a jihar ta ce tana binciken musabbabin gobara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel