Jami’an Tsaron Najeriya Sun Dura Kan ’Yan Bindiga a Jihar Arewa, Sun Kashe 18

Jami’an Tsaron Najeriya Sun Dura Kan ’Yan Bindiga a Jihar Arewa, Sun Kashe 18

  • Jami'an tsaro da suka hada da DSS, 'yan sanda da 'yan banga sun kai wani samame a mabuyar 'yan bindiga a jihar Filato
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron sun kai samamen a daidai lokacin da 'yan bindigar ke zaman tattaunawa da masu kai kwarmato
  • Wasu shugabannin matasa a karamar hukumar Wase da ke jihar sun ce samamen na zuwa makonni biyu da kai farmaki Zurak Campani

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Filato - Jami'an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), rundunar 'yan sanda da 'yan banga sun kai samame mabuyar 'yan bindiga a jihar Filato.

DSS, 'yan sanda da 'yan bijilan sun kashe 'yan bindiga a Filato
Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga 18 a jihar Filato. Hoto: @OfficialDSSNG
Asali: Twitter

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga 18

Akalla 'yan bindiga 18 aka kashe a harin wanda jami'an tsaron suka kai Zurak Campani da ke karamar hukumar Wase ta jihar a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga masallaci sun dauke masallata ana sallar dare a Jihar Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar rahoton Daily Trust, an kashe 'yan bindigar ne tare da masu kai masu kwarmato wadanda jama'a suka kama.

Wani shugaban matasa a Wase, Shafi'i Sambo, ya tabbatar da kai samamen, kuma ya ce jami'an tsaron hadin guiwar ne suka kashe 'yan bindigar.

Ya bayyana cewa an farmaki 'yan bindigar ne a lokacin da suke gudanar da wani taron tattaunawa a mabuyarsu.

'Yan bindiga sun kai hari Zurik

Wannnan samamen na zuwa makwanni biyu da 'yan bindiga suka kai farmaki yankin na Zurak Campani, inda suka kashe mutane bakwai.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun kai harin ne a wata kasuwar garin, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

A wannan samamen na ranar Litinin, shugaban matasan Wase ya ce:

"Lamarin ya faru misalin karfe 11 na dare, lokacin 'yan bindigar na taron tattaunawa. Jami'an DSS, 'yan sanda da 'yan bijilan ne suka kai samamen."

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a jihohi 2 na Arewa, sun lalata sansaninsu

"An kashe masu kai kwarmato" - Usman

Wani matashi a yankin, Abdullahi Usman, wanda ya tabbatar da kai samamen, ya ce:

"Bisa ga sahihan bayanai da jami'an tsaron suka samu, sun yi nasarar cimmasu a waje daya, kuma an kashe har da masu kai masu kwarmato."

Ko da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred domin jin ta bakin rundunar, bai amsa wayarsa ba kuma bai mayar da martani na sakon kar ta kwana da aka tura masa ba.

Yan bindiga sun kai hari jami'ar Taraba

A safiyar yau Talata ne Legit Hausa ta ruwaito cewa'yan bindiga sun kai farmaki jami'ar Taraba inda suka yi awon gaba da dalibai.

Kamar yadda jami'an tsaron jami'ar suka tabbatar, 'yan bindigar sun kai harin ne dakin kwanan dalibai, kuma sun tafi da dalibai biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel