Daukar Fansa: Mayakan ISWAP Sun Kai Wa Boko Haram Mummunan Farmaki a Tafkin Chadi

Daukar Fansa: Mayakan ISWAP Sun Kai Wa Boko Haram Mummunan Farmaki a Tafkin Chadi

  • Kungiyoyin 'yan ta'adda na ISWAP da Boko Haram sun yi wani kazamin fada a tsakaninsu, wanda ya yi silar mutuwar mutane da dama
  • Mayakan ISWAP ne suka kai farmakin ramuwar gayya a sansanin Boko Haram da ke Tumbun Jaki a ranar 21 ga watan Janairu
  • Wannan na zuwa ne yayin da matakan Boko Haram suka ki mika wuya a wani yunkuri da ISWAP ke yi na kwace masu muhalli

Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rikicin da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kungiyoyin 'yan ta'adda na Boko Haram da ISWAP, ba mai karewa ba ne nan kusa, yayin da bangarorin biyu ke tsara hanyoyin da za su iya wargaza juna.

Kara karanta wannan

An gano ramin karkashin kasa inda masu garkuwa suke ajiye wadanda suka sace a Najeriya

Fadan na baya-bayan nan da ya yi sanadin mutuwar mayaka da dama daga ko wane bangare ya faru ne a tsibirin Tumbun Rago na Tafkin Chadi.

Fada ya kaure tsakanin mayakan ISWAP da na Boko Haram
Tafkin Chadi: ISWAP ta kai wa Boko Haram harin ramuwar gayya, an kashe mutane. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Da sanyin safiyar ranar 22 ga watan Junairun 2024 ne mayakan ISWAP suka je inda mayakan Boko Haram suka yada zango a Tumbun Rago domin kai musu farmaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ISWAP ta kai farmakin matsayin ramuwar gayya

Farmakin, martani ne kan harin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a sansanin ISWAP da ke Tumbun Jaki a ranar 21 ga watan Janairu.

Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya samu rahoto daga majiya mai tushe cewa yakin da aka yi a Tumbun Rago ya yi sanadin zubar da jini yayin da kungiyar Boko Haram ta yi asarar rayuka da dama.

Ana hasashen za a ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin mayakan ISWAP da Boko Haram.

Kara karanta wannan

Rikici Tsakanin Boko Haram Da ISWAP Ya Yi Ƙamari Yayin Da Suka Kashe Juna a Sabon Rikici

'Yan Boko Haram a nasu bangaren, ba su shirya mika wuya ba, a wani yunkuri na mayakan da ISWAP ke yi na raba su da muhallansu.

Kotu ta daure matashin da ya karbi bashin banki ya kasa biya

A jihar Bauchi da ke Arewa maso gabashin Najeriya kuwa, kotu ta garkame wani Aminu Yusuf da ya karbi bashin naira miliyan 1.6 daga wajen bankin FCMB amma ya gaza biya.

An ruwaito cewa Yusuf ya karbi bashin ne da sunan zai bunkasa sana'ar sa, ashe karya ya yi, ya cinye kudin tas! Lamarin da ya sa EFCC ta gurfanar da shi gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel