Dattawan Kiristoci Sun Tona Asirin Masu Ingiza Ta'addanci a Najeriya, Sun Kawo Mafita

Dattawan Kiristoci Sun Tona Asirin Masu Ingiza Ta'addanci a Najeriya, Sun Kawo Mafita

  • Kungiyar Dattawan Kiristoci ta NCEF ta tona asirin wadanda ke jawo rashin zaman lafiya a Najeriya
  • Kungiyar ta ce wasu mutane ne daga kasashen ketare ke kawo matsalar tsaro da kashe-kashe a kasar
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Samuel Gani ya fitar yayin ganawa da manema labarai

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Dattawan Kiristoci a Najeriya (NCEF) ta bayyana wadanda ke jawo kashe-kashe a kasar baki daya.

Kungiyar ta zargi 'yan kasashen waje da kawo rashin tsaro a Najeriya da kuma tsattsauran ra'ayin addini, TheCable ta tattaro.

Dattawan Kiristoci sun nemo mafita kan matsalar tsaron Najeriya
Kungiyar Dattawan Kiristoci ta ce mutane daga kasashen ketare ke jawo matsalar tsaro a Najeriya. Hoto: Samuel Gani.
Asali: Facebook

Wace shawara kiristocin suka bayar?

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun yi martani kan lafta masu haraji a wani titin jihar Legas da Calabar

Shugaban kungiyar kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Taraba, Samuel Gani shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gani ya bukaci a yi zama na musamman tsakanin kabilun kasar domin kawo karshen matsalar da ake fuskanta.

Kungiyar ta ce kabilun kasar suna da abokan gaba daya wadanda suka fito daga ƙasashen waje, cewar rahoton Arise News.

Ta bukaci Shugaba Tinubu ya soke tsarin kiwon shanu a fili tare da kawo karshen shirin RUGA na Gwamnatin Tarayya.

Yawan mamaya da ake samu a Najeriya

"A kwanakin nan, wani shugaban al'umma a yankin Neja Delta ya yi korafin mamaya da ake musu."
"Haka nan an samu rahoton hakan a jihohin Adamawa da Taraba da Benue da kuma sauran yankunan Najeriya."
"Yan Najeriya ba su da matsala da juna, wasu ne daga ketare ke son lalata kasar domin kwace ta da kuma arzikinta."

Kara karanta wannan

Yayin da ya fara fitar da mai, Dangote ya samo mafita kan tsadar kayayyaki a Najeriya

"Lokaci ya yi da kungiyoyin Afenifere da Ohanaeze Ndigbo da Arewa Consultative Forum da PANDEF da kuma Middle Belt Forum za su zauna kan wannan matsala."

- Samuel Gani

Wannan na zuwa ne yayin da kar yawan samun kashe-kashe a kasar musamman a Arewacin Najeriya.

Kwankwaso ya fadi hanyar dakile matsalar tsaro

Kun ji cewa Sanata Rabiu Kwankwaso ya nuna damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara lalacewa a Najeriya.

Kwankwaso ya ce sojojin kasar suna da kwarewa da za su dakile matsalar gaba daya a kasar cikin sauki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.