Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Saƙo Bayan Kammala Ƙaramar Sallah a Najeriya

Sarkin Musulmi Ya Aike da Muhimmin Saƙo Bayan Kammala Ƙaramar Sallah a Najeriya

  • Sarkin Musulmi ya roƙi al'ummar musulman Najeriya su ci gaba da neman iimi kuma su yi wa shugabanninsu addu'a
  • Alhaji Sa'ad Abubakar na III ya aike da saƙon Barka da Sallah jim kaɗan bayan dawowa daga masallacin idi a jihar Sakkwato
  • Ya kuma buƙaci musulmai su ci gaba da taimakon juna da tausayawa juna a bayan watan azumin Ramadana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Sokoto - Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya taya ɗaukacin al'umma barka da Sallah yayin da musulman Najeruya suka gudanar da sallar idi ranar Laraba.

Sultan kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin shari'ar musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ja hankalin al'ummar musulmi su ci gaba da neman ilimi domin kyautata imaninsu.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnan Arewa ya faɗi alamun da ke nuna Allah SWT ya karɓi addu'o'in talakawa a Ramadan

Sultan Alhaji Sa’ad Abubakar.
Sultan ya buƙaci musulmai sun tashi su nemi ilimi kuma su yi wa shugabanni addu'a Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Twitter

Sarkin ya kuma buƙaci musulami su sanya shugabanninsu a addu'o'in su domin samun zaman lafiya mai ɗorewa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sultan ya aike da muhimmin saƙo

A sakonsa na Barka da Sallah ranar Laraba, Abubakar ya jaddada muhimmancin ci gaba da yi wa shugabanni addu’a da kuma samun kwanciyar hankali a ƙasa.

"Muna ƙara godewa Allah da ya raya mu cikin ƙoshin lafiya kuma ya bamu ikon yin azumi 30 da kuma yin idin Karamar Sallah.
"Yau rana ce mai muhimmanci a addinin muslunci yayin da al’ummar musulmi a fadin duniya ke murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma shagalin ƙaramar sallah (Eid-el-Fitr).
"Bugu da ƙari, ya kamata mu ci gaba da tausayawa da taimakon juna kamar yadda muka yi a watan Ramadana, sannan mu ƙara zage dantse wajen tallafawa mabuƙata."

Kara karanta wannan

Shugabanci: An faɗi wanda ya cancanci zama sabon shugaban jam'iyyar PDP daga Arewa

- in ji Sarkin.Musulmi.

Sarki ya yabawa gwamnan Sakkwato

Sarkin Musulmi ya yabawa gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu bisa jajircewa da aiki tare da malaman addinin Musulunci wajen hada kan al'umma.

Ya kuma yaba da kokarin gwamnati na tallafawa marasa galihu, ma’aikatan gwamnati, da kokarin dawo da tsaro da ci gaban jihar, rahoton Channels tv.

Sheikh Lukuwa ya bayyana dalilinsa

A wani rahoton kuma Malamin Musulunci, Sheikh Musa Lukuwa ya magantu kan dalilinsa na jagorantar sallar idi a jiya Talata 9 ga watan Afrilu.

Sheikh Lukuwa ya ce ya gamsu da ganin watan kasar Nijar inda ya ce babu dalilin ci gaba da azumi a watan Shawwal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel