Tsaro: Gwamnan Arewa Ya Faɗi Alamun da Ke Nuna Allah SWT Ya Karɓi Addu'o'in Talakawa a Ramadan

Tsaro: Gwamnan Arewa Ya Faɗi Alamun da Ke Nuna Allah SWT Ya Karɓi Addu'o'in Talakawa a Ramadan

  • Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya bayyana cewa alamu sun nuna Allah SWT ya karɓi addu'o'in neman zaman lafiya da mutane suka yi a Ramadan
  • Jim kaɗan bayan kammala sallar idi a Katsina, Gwamna Dikko ya ce tsaro ya kara inganta a faɗin jihar cikin ƴan kwanakin nan
  • Sarkin Katsina ya ja hankalin shugabanni da cewa su tuna wata rana Allah zai tambaye su kan nauyin mulki da ya ɗora masu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya yaba da addu’o’in da al'umma ke yi na neman zaman lafiya da ci gaban jihar.

Gwamna Dikko ya ce jihar Katsina ta samu ci gaba sosai a fannin tsaro na rayuka da dukiyoyin al'umma a ‘yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Ana fargabar mutane da yawa sun mutu yayin da jirgin sojoji ya jefa bam a filin idi a jihar Arewa

Gwamna Malam Dikko Radda.
Malam Radda ya fadi alamar da ke nuna Allah ya karbi addu'o'in Katsinawa a Ramadan Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook
"Wanda hakan na nuni da cewa Allah ya karɓi addu'o'in da muka yi a watan azumin Ramadana," in ji Radda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Dikko Radda ya yi wannan furucin ne jim kaɗan bayan kammala sallar idi ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu, 2024 a birnin Katsina.

Dandazon mutane ne suka halarci sallar idin wadda Imam Adam Husain ya jagoranta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sarkin Katsina ya tunantar da shugabanni

Sarkin Katsina, Dakta Abdulmumini Kabir Usman, ya tunatar da shugabannin siyasa cewa za su yi bayani dalla-dalla kan abin da suka yi a muƙamin da Allah ya ba su.

Sarkin ya yi kira ga al’ummar musulmi da su dukufa kuma su maida hankali wajen bautar Allah tare da taimakon juna a halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

Haka zalika a filin idin jami'ar Umaru Musa Yar'adua, limamin da ya jagoranci ƙaramar sallah, Dakta Muhammad Sagir Al-Madany, ya roƙi ƴan kasuwa su tausaya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya yi alkawarin cigaba da raba tallafi ga talakawa har bayan Ramadan

Malamin ya roƙi ƴan kasuwa su tausaya wa l'umma ta hanyar rage farashin kayayyakin amfani na yau da kullum tun da farashin Dala ya karye, rahoton Independent.

Yayin da Legit Hausa ta tattauna da wasu mazauna Katsina, sun bayyana cewa ba abin da za su ce kan tsaro sai dai su ƙara gode wa Allah.

Malam Yahuza ya fara da yabon Gwamna Dikko Raɗɗa, inda ya ce matakan da ya ɗauka a ɓangaren tsaro ne kaɗai hanyar magance matsalar.

"Gwamna yana matuƙar kokari kuma ka duba da yake magana sai ya miƙa lamarin hannun Allah. Tabbas Allah ne ya amshi addu'o'in mu kuma zamu ci gaba da roƙonsa."

Haka wani ɗan sa'kai da ya nemi a sakaya bayanansa, ya ce tabbas yanayin tsaron Ƙatsina ya inganta a halin yanzu.

Sultan ya ja hankalin musulmi

A wani rahoton na daban Sarkin Musulmi ya roƙi al'ummar musulman Najeriya su ci gaba da neman ilimi kuma su yi wa shugabanninsu addu'a.

Alhaji Sa'ad Abubakar na III ya aike da saƙon Barka da Sallah jim kaɗan bayan dawowa daga masallacin idi a jihar Sakkwato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel