Sallar Idi: Malamin Musulunci Ya Fadi Dalilansa Na Bijirewa Sarkin Musulmi, Ya Kawo Hujjoji

Sallar Idi: Malamin Musulunci Ya Fadi Dalilansa Na Bijirewa Sarkin Musulmi, Ya Kawo Hujjoji

  • Malamin Musulunci, Sheikh Musa Lukuwa ya magantu kan dalilinsa na jagorantar sallar idi a jiya Talata 9 ga watan Afrilu
  • Sheikh Lukuwa ya ce ya gamsu da ganin watan kasar Nijar inda ya ce babu dalilin ci gaba da azumi a watan Shawwal
  • Wannan na zuwa ne bayan malamin ya bijirewa umarnin Sarkin Musulmi tare da yin sallah sabanin sauran ‘yan Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto – Sheikh Musa Lukuwa ya kare kansa bayan jagorantar sallar idi a jihar Sokoto a jiya Talata 9 ga watan Afrilu.

Shehin malamin ya bijirewa umarnin Sarkin Musulmi kan ganin wata inda ya yi salla a jiya Talata 9 ga watan Afrilu, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami ya saɓawa Sarkin musulmi, ya yi sallar idin karamar Sallah a Sokoto

Malamin Musulunci ya fadi dalilin bijirewa Sarkin Musulmi
Sheikh Musa Lukuwa ya fadi dalilansa na bijirewa Sarkin Musulmi kan sallar idi a Sokoto. Hoto: Musa Dan Musa Richifa.
Asali: Facebook

Mene dalilan malamin na bijirewa Sarkin Musulmi?

Lukuwa wanda ya shafe shekaru ya na tawaye ga Sarkin Musulmin ya gabatar da sallar idi a Sokoto da misalin karfe 8:30 na safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da ya ke martani, Lukuwa ya ce an riga anga watan Shawwal a kasar Nijar wacce ke makwabtaka da Najeriya.

“Mun samu rahotanni da ke nuna cewa anga watan Shawwal a wurare da yawa har da nan Najeriya, amma wanda muka fi tabbaci shi ne a kasar Nijar.”
“Muna da faifan bidiyo ingantacce na malamansu da ke tabbatar da ganin watan inda kasar ta ayyana Talata 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar sallah.”
“Hakan shi ya ke tabbatar mana da cewa za a gudanar da salla ranar Talata saboda wannan shi ne koyarwar manzon Allah (SAW).”

- Sheikh Lukuwa

Kara karanta wannan

Bayan rashin ganin watan Ramadan, Tinubu ya sabunta ranakun hutun sallah a Najeriya

Malamin ya ce hakan sabawa Manzon Allah ne

Shehin malamin ya kara da cewa bai ga amfanin amincewa da Saudiyya ba idan har ba za a amince da kasar Nijar ba.

“Idan har za mu yarda da Saudiyya, me yasa ba za mu amince da na kasar Nijar ba wacce ke makwabtaka da mu.”

- Sheikh Lukuwa

Malamin ya dade ya na bijirewa Sultan inda ya ke zarginsa da tilasta Musulmai amincewa da ganin watan kasar Saudiyya wanda ya ce ya sabawa koyarwar manzon Allah (SAW), cewar Leadership.

Malamin Sokoto ya sake bijirewa Sarkin Musulmi

A baya, kun ji cewa Sheikh Musa Lukuwa ya sake bijirewa umarnin Sarkin Musulmi inda ya jagoranci sallar idi a Sokoto.

Sheikh Lukuwa ya jagoranci sallar idi ne a jiya Talata 9 ga watan Afrilu duk da rashin ganin wata da aka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel