Bayan Rashin Ganin Watan Ramadan, Tinubu Ya Sabunta Ranakun Hutun Sallah a Najeriya

Bayan Rashin Ganin Watan Ramadan, Tinubu Ya Sabunta Ranakun Hutun Sallah a Najeriya

  • Bayan rashin ganin watan Ramadan a Najeriya, Gwamnatin tarayya ta kara ranakun hutun bukukuwan sallah
  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da kara Alhamis 11 ga watan Afrilu a matsayin ranar hutun karamar sallah a kasar
  • Legit Hausa ta tattauna da wasu ma'aikatan Gwamnatin Tarayya kan karin hutun da Shugaba Bola Tinubu ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta kara ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu a cikin ranakun hutu domin gudanar da bukukuwan sallah.

Karin hutun kwana dayan bai rasa nasaba da rashin ganin wata a jiya Litinin 8 ga watan Afrilu a fadin Najeriya baki daya.

Tinubu ya kara ranar hutu a bayan rashin ganin watan Ramadan
Shugaba Tinubu ya kara Alhamis a matsayin ranar hutun sallah bayan rashin ganin watan Ramadan. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Yaushe ne karin ranar hutun sallah a Najeriya?

Kara karanta wannan

Eid-El-Fitr: Jerin gwamnonin jihohin Arewa da suka ayyana Jumu'a a matsayin ranar hutu

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar din-din-din a ma'aikatar harkokin cikin gida, Dakta Aishetu Ndayako ta tabbatar a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangarensa, Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji Ojo ya taya al'ummar Musulmai murnar kammala azumin watan Ramadan da bikin sallah.

Tun farko, Gwamnatin Tarayya ta ayyana yau Talata 9 ga watan Afrilu da gobe Laraba 10 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun bukukuwa salla.

Tattaunawar Legit Hausa da wasu ma'aikata

Legit Hausa ta tattauna da wasu ma'aikatan Gwamnatin Tarayya kan karin hutun da Tinubu ya yi

Aliyu Dauda da ke asibitin koyarwa ta Gwamnatin Tarayya ya ce wannan karin hutun zai ba ma'aikata damar sake shiri domin ci gaba ayyukansu.

Amma ya yi kira da a biya sauran kudaden rage radadin cire tallafi domin gudanar da hutun cikin walwala.

Kara karanta wannan

Yayin da ya fara fitar da mai, Dangote ya samo mafita kan tsadar kayayyaki a Najeriya

Mustapha Muhammad Biu da ke ma'aikatar makamashi a Abuja ya ce ya ji dadin karin hutun.

"Sai dai ba hutun ne kadai abin dubawa ba, akwai kudaden rage radadi wanda har yanzu ba a kammala biya ba."

- Mustapha Muhammad

Sallah: Ba a ga watan Ramadan a Najeriya ba

Har ila yau, Mai alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad na III, ya ayyana ranar Laraba 10 ga watan Afrilu, 2024 a matsayin ranar Sallah.

Sarkin Musulmin ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan rashin ganin jinjirin watan Shawwal a faɗin Najeriya a ranar Litinin 29 ga watan Ramadan.

An ba da hutun sallah a Najeriya

A baya, mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Talata, 9 ga wata da ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun bikin karamar Sallah.

Ministan cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ola shi ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel