Yadda Za Ku Warware Mas’alolin Sallar Idi Masu Rikitarwa, Sheikh Gidado Abdullahi

Yadda Za Ku Warware Mas’alolin Sallar Idi Masu Rikitarwa, Sheikh Gidado Abdullahi

  • Malamin ya bayyan yadda mutum zai warware matsaloli da suke bijorowa masallata a lokutan sallar idi
  • Yayi bayani akan muhimmancin sallar da kuma dalilan da yasa kowanne Musulmi kada yayi sakaci wajen halartar sallar
  • Ya kuma aika muhimmin sako ga iyaye a kan lura da yadda 'ya'yan su ya kamata su kasance a ranar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Sallar Idi sallah ce da ta bambanta da sauran sallolin da al'ummar musulmi su ka saba gudanar wa yau da kullum

Saboda haka ake yawan samun rudani a tsakanin masallata wanda warware su yakan bada wahala.

Taron maharata sallar idi da malam Gidado Abdullahi
Malamin ya warware mas'alolin sallar idi masu muhimmanci musamman wanda suka shafi kabbarori. Hoto: Jibwis Gombe/Gidado Abdullahi Asali: Facebook
Asali: Facebook

Sheikh Gidado Abdullahi, wani Malamin addinin a jihar Gombe ya warware manya daga cikin mas'alolin.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida ya aika sako, ya taya Kanawa murnar kammala azumin Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin addinin musuluncin ya warware mas'a'olin ne a shafin shi na Facebook, inda yake cewa:

Mas'alolin sallar idi a musulunci

Idan mutum ya samu liman yana karatun tahiya, zai zauna su yi karatun tare da liman, amma idan liman ya sallame zai tashi ya kawo raka'a biyu a siffar sallar Idi.

Idan kuma mutum ya samu liman ya kammala kabbori har ya fara karatu, zai fara da kabborin, idan ya gama kabborin sai ya saurari karatun liman.

Wani lokaci kuma mutum zai iya samun liman yana tsakiyar kabbarori, a wannan yanayin zai bi liman su karasa kabbarorin tare.

Bayan liman ya gama, sai ya kawo kabbarorin da suka wuce shi ko da liman ya fara karatu.

Idan kuma mutum ya samu liman yayi ruku'u, zai yi kabbarar harama ne kawai ya bi liman. A wannan yanayin babu bukatar kabbarori.

Kara karanta wannan

Bikin Sallah: DSS ta shawarci masallata yayin da ke shirin fita sallar karamar idi

Muhimmancin sallar Idi a Musulunci

Babban malamin ya ja hankalin al'umma a kan muhimmancin sallar Idi da matsayinta a addini.

Shehin yana cewa saboda muhimmancin sallar ne Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya bada umarni a rika yinta.

Ya kara da cewa saboda muhimmancin sallar ne ma ake bawa ma'aikata hutu domin su samu halartar ta.

Su waye ya kamata su halarci sallar Idi?

Sheikh Gidado ya bayyana cewe Shari'a ta halastawa kowa zuwa sallar Idi. Maza da mata da kananan yara, har mata marasa tsarki idan sun je sai su yi nesa da wurin sallah.

Dangane da fitan mata da yara zuwa idi

Malamin ya ja hankalin iyaye akan su kula da sutura da mata da yara zasu saka yayin halartar sallar.

A cewar shi, bai kamata a barsu suna yin shiga data sabawa koyarwar addini ba.

Gobe za'a yi sallar Idi a Najeriya

Kara karanta wannan

Sauyin yanayi: Tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 za su samu aiki da gwamnatin tarayya

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad na III, ya bada sanarwar cewa gobe Laraba ne za'a yi sallar Idi a fadin Najeriya.

Sanarwar tazo ne bayan rashin ganin watan Shawwal a yammacin Litinin, hakan kuma yana nufin azumi talatin za'ayi bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel