Abba Gida Gida Ya Aika Sako, Ya Taya Kanawa Murnar Kammala Azumin Ramadan

Abba Gida Gida Ya Aika Sako, Ya Taya Kanawa Murnar Kammala Azumin Ramadan

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya kanawa da sauran musulmi murnar kammala azumin watan Ramadana da aka shafe kwanaki 30 ana yi
  • A sanarwar da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Yusuf ya yi kamata ya yi mussulmi su yi riko da kyawawan halayen da suka koya
  • Ya yi alkawarin ci gaba da tafiyar da gwamnatinsa domin wanzuwar zaman lafiya da kwaniyar hankali a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kano- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya taya al'ummar musulmi kammala azumin watan Ramadan.

Mai girma gwamnan ya kuma taya su murnar sallah ƙarama da za a fara a Larabar nan.

Kara karanta wannan

Gwamna Yusuf ya Sake Nada Hadimin da ya yi Barazana ga Rayuwar Alkalan Zaben Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya taya musulmi murnar zagayowar sallah Karama
Gwamnan Kano ya yi fatan musulmi za su ci gaba da riko da halayen kirkin da suka koya a Ramadana Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Wannan na ƙunshe ne a saƙon taya murnar sallah ya mai magana da yawunsa,Sunusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yayin da watan azumin Ramadana ya zo ƙarshe, yanzu an ga watan Shawwal, halayyar son juna, da kyauta, sanin ya kamata, kishin ƙasa da zaman lafiya da mu ka koya a watan ya kamata mu riƙe shi domin samun zaman lafiyar da mu ke so."

Ya hori Kanawa su yi addu'ar samun taimakon Allah ga shugabanninsu a kowane matakin.

Gwamna Yusuf ya kuma yi wa al'umarsa alƙawarin tafiyar da gwamnati yadda za a samu kwanciyar hankali da zaman lafiya.

An bayyana gobe ranar Sallah

A ranar Litinin ne mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya bayyana cewa za a yi sallah ranar Laraba.

An cimma matsayar ne bayan jaririn watan Shawwal bai bayyana a sararin Subhana ba a yammacin Litinin ɗin.

Kara karanta wannan

Fitaccen malami ya saɓawa Sarkin musulmi, ya yi sallar idin karamar Sallah a Sokoto

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin kula da harkokin Musulunci na fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu, a gobe Laraba ne za a yi sallah.

Abubuwan da musulmi zai yi ranar sallah

Ana ajiye azumin watan Ramadan aka ji cewa musulmi zai fara wasu ayyukan ibada domin neman yardar Ubangiji Madaukakin Sarki.

Daga cikin abbubuwan da zai yi akwai kabarbari, da ambaton Allah har ranar Idi baya ga zakkar fitar da kai da ake rabawa mabukata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel