Goron Sallah: Kyawawan ladubban sallar Idi guda 14
A daren litinin, 3 ga watan Yuni ne mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya sanar da ganin jinjirin wata a wasu yankunan Arewacin Najeriya, wanda hakan ya kawo karshen azumin watan Ramadana, kuma ya shigar da Musulmai 1 ga watan Shawwal, ranar Sallah.
Legit.ng ta ruwaito akwai wasu kyawawan ladubba da suka samo asali daga adinin Musulunci, wadanda ake bukatar duk wani Musulmi ya mu’amalantu dasu, sune kamar haka;
KU KARANTA: Likafa ta cigaba: An samu zababben Sanata dan Kwankwasiyya a kasar Gambia
- Farkawa daga barci da wuri da samun sallar Asubah
- Wankan tsarki
- Tsaftace baki
- Sanya tufafi mafi kyawu
- Fesa turare mai kamshi
- Halartar filin Idi cikin lokaci
- Cin dabino, marra marra
- Canza hanyar zuwa Masallaci dana dawowa
- Tafiya a kasa
- Karanta zikirin “Allahu Akbar Allahu Akbar, La’ilaha ilallah, Allahu Akbar Allahu Akbar, walillahil hamd”
- Samun Sallar Idi
- Bayar da Zakkar fidda kai
- Sauraron kudubar limamin Idi
- Ziyarar yan uwa da abokan arziki
Da fatan Allah Ya karbi kyawawan ayyukan da Musulmai suka yi a yayin azumin watan Ramadana, Ya kuma basu ladar aikatawa, Amin.
A hannu guda kuma ana tunatar da wanda ya samu dama cewa akwai azumin nafila guda shida da anso Musulmi yayi a cikin wannan wata na Shawwal, shima azumin na dauke da gwaggwabar lada.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng