Yan Sanda Sun Kama Mutane Sama da 100 Bisa Zargin Aikata Wasu Laifuka a Jihar Kano

Yan Sanda Sun Kama Mutane Sama da 100 Bisa Zargin Aikata Wasu Laifuka a Jihar Kano

  • Dakarun ƴan sanda sun yi nasarar cafke mutane 120 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar Kano a watan Maris
  • Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce daga cikin waɗanda aka kama har da masu garkuwa da mutane
  • Kiyawa ya ce jami'an sun kuma kwato kayayyaki masu yawa daga hannun ɓarayin da aka kama da suka haɗa da babura da motoci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Juma’a ta ce jami’anta sun kama mutane 120 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a cikin watan Maris.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a manhajar X watau Twitter.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 19 a wani sabon hari a jihar Arewa

Kwamishinan ƴan sandan Kano, Gumel.
Yan sanda sun samu gagarumar nasara a watan Maris Hoto: @KanopoliceNG
Asali: Twitter

A sanarwar da ya fitar da yammacin Jumu'a, Kiyawa ya ce mutanen da aka kama sun hada da ƴan fashi da makami 15, masu garkuwa da mutane 4 da kuma wasu 10 da ake zargin dillalan kwayoyi ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kazalika an kama wasu barayin motoci 4, barayin adaidaita sahu 3, barayin babura 7, ƴan damfara 2, barayi 20, da kuma 55 da ake zargin ƴan daba ne.

Kiyawa ya kuma bayyana cewa rundunar ta tarwatsa matsugunan masu garkuwa da yawa tare da ceto wadanda aka yi garkuwa da su da kwato kayan aikinsu.

Ƴan sanda sun kwato kayayyaki

Sauran kayan da ƴan sanda suka kwato sun hada da harsashi guda 15 na AK-47, harsashi guda 12 masu nauyin 7.62mm, bindigogin gida guda 24, motoci 7, Keke napep 3, babura 5, da wukake 28.

Kara karanta wannan

Dala ta yi muguwar faɗuwa, ta dawo ƙasa da N700 a Najeriya? Gaskiya ta bayyana

"Rundunar ‘yan sanda a tsakanin ranakun 1 zuwa 31 ga Maris, 2024, ta kara kaimi tare da aiwatar da tsare-tsare domin magance ‘yan daba a wasu wuraren da aka gano a cikin jihar musamman birni.
"Wasu daga cikin wadannan dabarun da aka yi amfani da su sun hada da daukar aikin 'yan sanda da dabara ta aiki, tare da kafa karin rukunin yaƙi da daba a Dorayi."

- Abdullahi Kiyawa.

Rikici ya barke da ƴan shi'a

A wani rahoton kuma Jami'an ƴan sanda da ƴan shi'a sun yi arangama ranar Jumu'a, 5 ga watan Afrilu, 2024 yayin da suka fito muzaharar ranar Quds a Kaduna.

Ƴan shi'ar sun fito da yawa a Kaduna amma ƴan sanda suka yi ƙoƙarin tarwatsa su saboda wasu daga cikin suna ɗauke da makamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel