Binciken Ganduje: Kwankwaso Ya Shiga Matsala Bayan APC Ta Bankado Wata Badakala

Binciken Ganduje: Kwankwaso Ya Shiga Matsala Bayan APC Ta Bankado Wata Badakala

  • Yayin da aka kafa kwamitin bincike kan Abdullahi Ganduje, APC ta shawarci kwamitin bincike kan wanda ya kamata a fara tuhuma
  • Shugaban jam'iyyar a Kano, Abdullahi Abbas ya ce Rabiu Kwankwaso ya kamata a bincika kan siyar da kadarorin gwamnatin kaso 70
  • Ya ce Kwankwaso ya yi badakala yayin da ya ke mulki daga 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015 a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Shugaban jami'yyar APC a Kano, Abdullahii Abbas ya ba kwamitin bincike shawara kan wanda ya kamata su fara bincika a jihar.

Abba ya ce babu wanda ya cancanci a fara bincika kamar tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Kwankwaso saboda ya siyar da kaso 70 na kadarorin jihar ga iyalansa da abokai.

Kara karanta wannan

NERC ta tsokano ‘yan kwadago, ana yi wa Tinubu barazana saboda kudin lantarki

Yayin da za a fara binciken Ganduje, APC ta bankaɗo badakalar Kwankwaso a Kano
APC ta bankaɗo badaƙalar Rabiu Kwankwaso yayin da aka kafa kwamitin binciken Abdullahi Ganduje. Hoto: @OfficialAPCNg, @KwankwasoRM.
Asali: Twitter

Wane zargi APC ke yi kan Kwankwaso?

Shugaban jam'iyyar ya ce ya kamata ya yi kwamitin ya fara bincike daga 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Asabar 6 ga watan Afrilu a Kano, cewar rahoton Vanguard.

Ya ce karkatar da kadarori gwamnati a wancan lokaci ya faru ne a idon Gwamna Abba Kabir lokacin ya na kwamishinan ayyuka.

APC ta zargi mambobin NNPP a cikin kwamitin

Ya kuma yi fatali da yadda aka kafa kwamitin bincike wanda ya kunshi 'yan jam'iyyar NNPP da sauran 'yan siyasa, cewar Premium Times.

"Wannan aiki da aka fara ya nuna yadda gwamnati ta mayar da hankali kan bita da kullin siyasa game da wannan bincike."
"Daga 2011 zuwa 2015, ayyukan hanya na kilomita hudu a kananan hukumomi 44 an ba da kwangila aikin amma daga bisani aka karkatar da kudin ba tare da yin aiki ba."

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Ganduje ya magantu kan binciken da gwamnatin Kano za ta yi masa

"A wancan lokaci, an ba da ayyukan N3bn amma Kwankwaso ya karkatar da su yayin kamfen shugaban kasa a Legas."

- Abdullahi Abbas

Sabbin zarge-zarge sun bayyana kan Ganduje

Kun ji cewa an gano wasu takardun kotu da ke zargin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da badakala a kamfanin auduga.

Takardun sun zargi Ganduje da siyar da kamfanin auduga da ke Challawa ga iyalansa ba tare da saka kudin a asusun gwamnatin jihar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel